1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yau aka cika shekaru 16 da sake hade Jamus ta Gabas da Ta Yamma

October 3, 2006
https://p.dw.com/p/BuhW
A yau talata tarayyar Jamus ke bukin cika shekaru 16 da sake hadewar yankin Gabashin kasar mai bin tsarin kwaminisanci da na yamma mai bin tsarin jari hujja. Ana sa ran cewa dubun dubatan mutane zasu hallara a birnin Kiel dake arewacin kasar, inda a bana shugaban kasa Horst Köhler da SG Angela Merkel zasu jagoranci bukuwan da za´a gudanar. A kuma halin da ake ciki ministan dake kula da aikin raya jihohin gabashin Jamus, Wolfgang Tiefensee ya ce duk da ci-gaban da aka samu a cikin shekaru 16 da suka gabata, za´a dauki shekaru 15 zuwa 20 nan gaba jihohin gabashin kasar na dogaro kan na yamma musamman dangane da taimakon kudi. A kuma yau din ne masallatai kimanin dubu daya a fadin tarayyar ta Jamus zasu gudanar da ranar bude kofofinsu ga maziyarta wadanda ba musulmi ba, inda za´a yi nune-nune da bayyanai akan addinin musulunci. Majalisar tsakiya ta al´umar Musulmi a nan Jamus wadda ta fara wannan shiri shekaru 10 da suka wuce ta ce ranar bude kofofin masallatan shi ne irinsa na farko a duk duniya baki daya. Alkalumman hukuma sun yi nuni da cewa akwai masallatai kimanin dubu 2 da 300 a fadin Jamus baki daya.