1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yau ake bukin ranar yaki da bautar da kananan yara na duniya

June 12, 2007
https://p.dw.com/p/BuJ9
MDD ta ce yaki da talauci a kasashe masu tasowa shi ne babban makamin yaki da bautar da kananan yara. A cikin wata sanarwa da ta bayar yau ranar yaki da kwadagon kananan yara na kasa da kasa, kungiyar aikin noma da samar da abinci ta MDD wato FAO ta ce muhimmin abu shi ne a dauki sahihan matakan rage talauci musamman a yankunan karkara na kasashe masu tasowa. Alkalumma sun yi nuni da cewa a duniya baki daya akwai kananan yara miliyan 218 da ake tilasta musu yin kwadago. Miliyan 132 daga cikin su kuwa ana bautar da su ne a gonaki.