1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

041108 USA Wahltag

Engelke, Anna, Washington (WDR) November 4, 2008

Ana takara ne tsakanin Obama na jam´iyar Demokrats da McCain na jam´iyar Republicans.

https://p.dw.com/p/FnH8
John McCain da Barack ObamaHoto: AP Graphics/DW

Yau ce ranar yanke hukunci a Amirka inda yanzu haka ake cikin kaɗa ƙuri´a a zaɓen shugaban ƙasar. Shin ko Amirkawa za su zaɓi baƙar fata a matsayin shugaban ƙasar a karon farko? Sakamakon ƙuri´ar jin ra´ayin jama´a ta ƙarshe da aka gudanar gabanin zaɓen na yau, kashi 53 cikin 100 na Amirka na goyon bayan Barack Obama a matsayin sabon shugaba yayin da kashi 42 cikin 100 ke son ɗan jam´iyar Republicans John McCain.

Da kyau kasancewar a yau ake gudanar da zaɓen domin an rigaya an samu dukkan bayanai da ake buƙata game da zaɓen na Amirka. Alal misali an san cewa idan aka yi ruwan sama a ranar zaɓe to kashi ɗaya cikin 100 na Amirkawa za su yi zaman su ne a gida. Wani Farfesa a jami´ar Georgia ya gano haka bayan nazarin da yayi akan zaɓaku 14 da suka gabata. Ya kuma gana cewa idan aka yi ruwan sama zai dagulawa Obama lissafi.

Wani mai hasashen yanayi a tashar telebijin ta CNN ya rawaito wani Farfesa na cewa idan aka yi ruwan sama a yau kashi 2.5 cikin 100 na magoya bayan jam´iyar Democrat ba za su fita kaɗa ƙuri´a ba.

A jiya Litinin dukkan ´yan takarar biyu sun yi kira ga magoya bayansu da ka da su zauna gida. Ga dai abin da Obama ya faɗa a jihar Florida.

"Ba za mu nuna gajiyawa ba ba za mu yarda mu zama ´yan kallo ko na kwatankwacin ƙwayar zarra ba. Ba za mu yi sake a wannan lokaci mai muhimmanci ba. Dole ne mu yi nasara a Florida da wannan zabe gaba ɗaya."

Jihohi uku Obama ya yi yaƙin neman zaɓensa na karshe a jiya, inda da dare ya samu labarin rasuwar kakarsa bayan ta yi fama da cutar kyansa. A makonni baya Obama ya katse yaƙin neman zaɓe inda ya kai mata ziyarar da ta zama ta bankwana a Hawaii. Yanzu da rai ya yi halinsa ba za ta shaida ba ko jikanta zai zama shugaban Amirka karo na 44. A ƙuri´ar jin ra´ayin jama´a a ƙasa Barack Obama na gaban John McCain da kimanin kashi biyar zuwa 11 cikin 100. To sai dai muhimmin abu a ƙarshe shi ne sakamakon zaɓe a ɗaiɗaikun jihohin tarayya. Domin ɗan takara na iya zama shugaba ƙasa ne idan ya samu aƙalla ƙuri´u 270 na waɗanda za su zaɓi shugaban Amirka. A nan ma dai Obama ke kan gaba, to sai dai McCain baya son jin haka kamar yadda ya nunar a yaƙin neman zaɓe a Pennsylvania.

"Ya saura kwana guda kafin mu bawa Amirka sabuwar alƙibla. Dole mu yi nasara a Pennsylvania. Za mu samu wannan nasara tare da taimakonku. Don Allah ku fita ƙwanku da kwarkwatarku don kaɗa ƙuri´a. Ina buƙatar ƙuri´unku."

Mutanen da ke kaɗa ƙuri´arsu a wannan karo su ne mafi yawa a cikin tarihin Amirka. Alƙalumman sun yi nuni da cewa mutane miliyan 153 za su sauke wannan farali wato kimanin kashi 74 cikin 100 na waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri´a a Amirka. Saboda haka ba abin mamaki ba ne da ake bayyana zaɓen da cewa na tarihi ne.