1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yau ce rana ta biyu a ziyarar Paparoma Benedict na 16 a Turkiya

November 29, 2006
https://p.dw.com/p/BuZo

A rana ta biyu a ziyarar da yake kaiwa kasar Turkiya a yau laraba Paparoma Benedict na 16 zai ziyarci garin Ephesus inda zai jagoranci wani bukin addu´o´i. Bisa ga riwayar darikar Katholika a wannan gari ne Maryam mahaifiyar annabi Issah (ASW) ta yi zama kimanin shekaru dubu 2 da suka gabata. A lokacin da ya isa a birnin Ankara jiya shugaban na mabiyar darikar Katholika a duniya ya yi kira da karfafa tattaunawa tsakanin al´umar Kirista da musulmi. A cikin wani jawabi da yayi a gaban jami´an diplomasiya Paparoma ya yi kashedi da ka da a yi amfani da addini wajen aikata tarzoma da tashe tashen hankula. A dangane da zanga-zangar da al´umar Turkiya ke yi don adawa da wannan ziyara, an tsaurara matakan tsaro a dukkan wuraren da Paparoma zai yi rangadi a cikin kasar.