1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yau hukumar kungiyar EU zata yi na´am da daukar Bulgaria da Romania cikin EU

September 26, 2006
https://p.dw.com/p/BuiG
A yau talata hukumar KTT zata gabatar da rahoton ta dake nuni da irin ci-gaban da aka samu a tattaunawar da ake yi da nufin daukar kasashen Bulgaria da Romania a cikin kungiyar EU. Rahotanni sun nunar da cewa bisa ga dukkan alamu rahoton zai amince da daukar kasashen biyu cikin kungiyar a ranar daya ga watan janerun shekara mai zuwa. To amma majiyoyin ´yan diplomasiya sun ce hukumar zata gindaya sharudda masu tsauri game da daukar kasashen cikin kungiyar. Daga cikin sharuddan har da wasu matakai wadanda zasu amince da sa ido kan ci-gaban da kasashen biyu ke samu a sauye sauyen da suke aiwatarwa a tsarin shari´a da kuma yaki da cin hanci da rashawa. Shugabannin kasashen kungiyar ta EU dai ne ke da ikon yanke shawara ta karshe game da daukar kasashen.