1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yau wakilin Majalisar Ɗinkin Dunia Ibrahim Gambari zai ziyarci Myanmar

September 29, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9x

Yau ne wakilin mussamman na Majalisar Dinkin Dunia a ƙasar Myanmar Ibrahim Gambari, zai sauka a Rangoon babban birnin ƙasar, inda ake kyauttata zaton zai gana da hukumomi ,a game da tashe-tashen hankulan da ke ci gaba da wakana.

Masu zanga-zangar sun sha alwashin sake fitowa a titina, a yau asabar, a yayin da sojoji, ɗauke da mayan makamai su ka ja daga a cikin titinan, tare da umurnin hanna zanga zangar ta ko wane hali.

Rahotani daga ƙasar sun ce, fiye da mutane 20 su ka rasa rayuka, sannan wasu da dama su ka ji raunuka a cikin arangama da jami´an tsaro.

A ɗaya wajen, sojoji sun kame da dama daga shugabanin wannan zanga-zanga.

ƙasashe da ƙungiyoyi daban daban na dunia, na ci gaba da matsa ƙaimi ga gwamnatin mulkin sojan ƙasar Myanmar, domin ta saurari koke-koken masu zanga-zangar da kunuwan basira.

A wannan ziyara Ibrahim Gambari na da burin ganawa da madugun yan adawar ƙasar, Aung San Su Kyi, da shugaban mulkin soja Than Shwe, ya kafawa dokar hana zirga zirga.