1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaushe shugaban ƙasar Libiya Muhammar Ƙhaddafi ya hau mulki?

September 9, 2010

Taƙaitacen tarihin shugaban ƙasar Libiya Kalan Muhammar Ƙhaddafi da rawar da ya taka a jagorancin ƙasar.

https://p.dw.com/p/P7y3
Kalan Muhammar Kaddafi shugaban LibiyaHoto: AP

An haifi Muhammar Ƙhaddafi ranar 19 ga watan Juni na shekara 1942 a garin Syrte na ƙasar Libiya.Shi ne ɗan auta a gidansu, kuma ya fito daga ƙabilar makiyaya ta Bedouin   da ke cikin dajin Saharan Libiya.Ya fara karatun firamari a makarantar Sebha da ke yankin Fezzan.

Tun daga cikin wannan makaranta, tare wasu samari abokansa, su ka fara tunanin yadda za su ɗauki mulkin ƙasar Libiya idan sun girma.Tunanin Ƙhadafi ko yaushe shine ta yaya zai zama kamar shugaban ƙasar Misira Gamal Abdel Naser.

A shekara 1961 a ka kore shi daga makarnatar Sebha dalili da tsageranci da tada zaune tsaye.

Duk da haka dai, ya ci gaba da karatu, inda har ya shiga jami´ar Libiya ɓangaren ilimin shari´a da dokoki.

Daga nan kuma ya shiga makarantar koyan aikin soja da ke birnin Benghazi a shekara 1963, inda anan ma ya ci gaba da tunanin yadda zai kifar da masauratar Libiya.Bayan ya yi shekaru biyu cikin wannan makaranta sai aka tura shi Ingila, inda ya yi karatun soja na tsawan shekara ɗaya.Sakamakon wannan karatu ya zama kaftan a cikin rundunar sojojin Libiya.

Kaftan Ƙhaddafi ya kifar da Sarki Idris na ɗaya ,ranar 1 ga watan Satumba na shekara 1969, a lokacin da Sarkin ya na ƙasar Turkiya wurin jinya.Daga wannan rana sojojin da suka shirya juyin mulki su ka rusa mulkin sarautar galgajiya a Libiya su ka ƙaddamar da Jamhuriya.Kuma daga rannan ne, daga galar Kaftan, Ƙhadafi ya naɗa kansa Kalan, matsayin da ya riƙe da shi har yanzu.

Tun lokacin da ya hau karagar mulki ya ƙaddamar da aƙidar juyin juya hali ta hanyar bayyana tsantsan kishin ƙasa.Saboda haka ya buƙaci kamfanonin ƙasashe ƙetare kamar su Italiya da su yi kaka gida a Libiya su tattara yanasu-yanasu su fice daga ƙasar.

Sannan ya buƙaci Amurika ta kwashe sojojinta da ke Libiya.

A wani mataki an kare Libiya daga hare-hare shugaba Khaddafi ya bayyana aniyarsa ta ƙera makaman ƙare dangi, abinda ya sami tofin Allah tsine daga ƙasashen yammacin duniya.

A shekara 1970 babu zato babu tamahha Kalan Ƙhadafi ya ƙara kuɗin man petur, matakin da ya haddasa ruɗami a kasuwanin ɗanyan mai na duniya.

Sannan ƙasashen yamma na zargin sa da ɗaurewa ta´adanci da ´yan ta´ada gindi, bayan hare haren jiragen sama na Lockerbie da kuma na DC-10  UTA  a sararin samaniyar Sahara Jamhuriya Niger a shekara 1988, wanda su ka yi sanadiyar mutuwar ɗaruruwan mutane.

Tsakanin Faransa da Libiya kuma akwai taƙƙadama itama da ta kunno kai bayan da a shekara 1973 shugaba Ƙhadafi ya mamaye zirin Aozou na ƙasar Tchadi.Saboda haka, Faransa ta aika tawagar sojojin domin kariya ga ƙasar Tchadi da ta yi wa mukin mallaka.

Wasu kenan daga hujjojin da suka sa ƙasashen yammacin duniya su ka kafa ƙafon zuƙa ga shugaban Libiya.

saboda haka ranar 15 ga watan Afrilu na shekara 1986,shugaban Amurika  Ronald Reagan ya umurci sojojin Amurika su kaiwa Mohamar Ƙhaddafi hari domin su hallaka shi. Sun hauda wata tawagar soja da su ka raɗawa suna El Dorado Operation.

Tawagar sojojin ta kai hare ja´hare a Benghazi da Tripoli, sai dai ba ta yi nasara kashe Khaddafi ba illa kawai dai ya sami rauni.

Amma a jimilce sojojin Libiya 45 da fara hula 15 su ka rasa rayuka cikin wannan tagwayen hare-hare,daga cikin su har da Hannah wata yarin ya da Ƙhaddafi ke riƙo.

Dalilin kai wannan shine maida martani ga tarwatsewar bam da ake zargin Libiya da aikatawa a cikin wani gidan rawa na birnin Berlin a nan Taraya Jamus, ranar 5 ga watan Afrilu na shekara 1986.Sojan Amurika ɗaya ya mutu a cikin harin.

A lokacin zaman gabar Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran manyan ƙasashen duniya, sun saka takunkumi ga Libiya.Kuma yanzu duniya ta kasance tamkar wani ɗan ƙaramin gari, inda babu ƙasar da za ta iya rayuwa ita kaɗai ba tare da cuɗe ni in cuɗe ka ba da sauran ƙasashen duniya.

Saboda haka a wajejen shekara 1990, Mohamar Ƙhaddafi ya fara tunanin sake ƙulla ma´amala tsakanin ƙasarsa da sauran manyan ƙasashen duniya.

Saboda a shekara 1999 ya miƙawa kotun Scottland jami´an da a ke zargi da aika harin jirgin Lockerbie,da na DC-10 UTA, har ma Libiya a amince ta biyya diyyar dala miliyan fiye da dubu biyu ga iyalen mutanen da su ka mutu a harin Lockerbie.

 A sakamakon hakan, Majalisar Ɗinkin Duniya ta cire takunkumin da ta ƙargamawa Libiya.

Kazalika,a farkon shekara 2003, ƙhaddafi ya shiga tattanawa da Amurika da Birtaniya, inda su ka cimma yarjejeniyar yin watsi da ƙera makaman  nukiliya inda har ma Libiya ta rattaba hannu akan yarjejeniyar ƙasa da ƙasa da haramta wannan makamai.

Bayan Amurika da Ingila Ƙhadafi ya maida hulɗoɗin diplomatiyya da ƙasashe kamar su Faransa Italiya Spain da sauransu.

A halin da ake ciki yanzu, duk da cewar  ana zama irin na "ta ciki na ciki "tsakanin Khadafi da ƙasashen yammacin duniya, amma a na damawa da Libiya a dandalin diplomatiyya na duniya.Hatta a baya-bayan nan sai da ya kai ziyara aiki a ƙasar Italiya.

Kalan Ƙhaddafi na da ´ya´ya takwas:

Babban su shine Mohamed Ƙhaddafi, wanda ya samu da matarasa ta farko,Kuma a yanzu shine shugaban hukumar sadarwa ta ƙasar Libiya.

Akwai Seif el-Islam shugaban gidauniyar Ƙhaddafi.

Shine babban a ɗakin Safia matar Ƙhadafi ta biyu.

Seif el -Islam ya fi sauran shiga harakokin siyasar Libiya.

Akwai Saadi, wanda shahararen ɗan ƙwallo ne kuma soja ne a yanzu ya na jagorancin wata bataliyar sojoji.

Sai kuma Moatassem Billah wanda tun shekara 2007 ya ke jagorancin komitin tsaro na ƙasa.

Sai kuma Hannibal wanda shima soja ne kuma likita.

Akwai Aisha wadda iat lauya ce.

Bayan ta sai Seif el-Arab, sannan ɗan auta Khamis.

Mawallafi: Yahouza Sadisou Madobi 

Edita: Ahmed Tijani Lawal