1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan Al'ummar Duniya

Abba BashirApril 24, 2006

Yawan Al'ummar Duniya a kiyasce

https://p.dw.com/p/BvVV
Hoton Duniya
Hoton DuniyaHoto: Google Earth

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon,ta fito ne daga hannun Malama Lubabatu Sulaiman Ado,daga Karamar hukumar Nassarawa dake Jihar Kanon tarayyar Najeriya. Malamar tace ,shin don Allah nawa ne yawan Al’ummar dake fadin Duniyar nan ne ?

Amsa: To Malama Lubabatu,kamar yadda kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nunar,tare da hadin gwiwar hukumar kidayar Al’umma ta kasar Amurka,sun bayyana cewar,a Kiyasce yawan Al’ummar Duniya,ya kai kimanin Mutane Biliyan 6,499,697,060.

Idan kuma aka koma ga yawan yadda Al’ummar Duniya ke karuwa, kididdigar tayi nuni da cewar ana haihuwar akalla Mutane dubu 358,522 wato dai a kowanne minti daya ana haihuwar mutanen da yawansu ya kai 249 a ilahirin fadin wannan duniya tamu.Ta bangaren Rasuwa kuwa, an kiyasta cewar,a kowacce rana ta Allah,mutane 155,012 ne ke danganawa da gidan gaskiya,wato kenan a kowanne minti daya Mutane 108 ne suke shekawa barzahu.Amma duk da haka kididdigar ta yi nuni da cewar,yawan Al’mmar Duniya a yanzu haka ,ya ninka yawan da ake da shi a shekaru 42 da suka wuce.

Kididdigar dai har ila yau ta bayyana cewa,Mutanen da aka haifa kuma suka rasu a shekaru 600,000 da suka wuce, yawan su ya kai kimanin Mutane Biliyan 75,000,000,000.

Aiki sai mai shi.Tsarki ya tabbata ga Allah gwani wajen halitta.