1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan bakin haure a Jamus na karuwa

Zulaiha Abubakar
April 12, 2018

Kakakin hukumar kididdigar yawan al'umma ta kasar Jamus, ya sanar da cewar a halin  yanzu yawan bakin haure a kasar  ya karu da sama da kaso.

https://p.dw.com/p/2vwIx
Griechenland Mazedonien Flüchtlinge bei Idomeni
Kwararar bakin haure da 'yan gududn hijira zuwa JamusHoto: Getty Images/M. Cardy

Sanarwar ta kara da cewa bisa wani bincike da hukumar ta gudanar a karshen shekarar da ta gabata, ya nunar da cewa akwai mutane miliyan 10 da ke zaune a kasar, wadanda suka fito daga wasu kasashen kuma suka samu shaidar zama a kasar Jamus. Koda yake kididdigar ta bayyana samuwar raguwar bakin da suka fito daga kasashen da ba na Tarayyar Turai ba wadanda suka hada da kasar Siriya da Iraki da kuma Afghanistan.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Jamus ke fuskantar kwararar sabbin baki daga kasashen nahiyar Turai musamman ma gabashin Turai da kaso 12. Yawan al'ummar da ke Jamus ya fara karuwa ne tun a shekara ta 2007, lokacin da aka samar da damar cin moriyar shige da ficen al'ummar gabashin Turai.