1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan mutanen da suka rasu a girgizar ƙasa a Indonesia ya kai 17

September 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuBQ
Ma´aikatan ceto a Indonesia na ci-gaba da kai dauki cikin gaggawa a fadin yankin Sumatra inda a halin yanzu yawan wadanda suka rasu sakamakon mummunan girgizar kasar da ta auku ya kai mutum 17. Jami´ai sun ce an kai abinci da sauran kayan agaji ga yankuna da dama da girgizar kasar ta shafa to amma ana bukatar karin tantuna ga mutanehn da ke kwana filin Allah Ta´ala. A jiya juma´a an sake yin wata girgizar kasar a Sumatra wadda ta razana dubun dubatan mutane da suka ki komawa gidajensu dake gabar teku bisa tsoron aukuwar igiyar ruwa ta Tsunami. Masana na fargabar sake aukuwar mummunar igiyar ruwa ta Tsunami shigen wadda ta auku a shekara ta 2004 wadda ta halaka mutane sama da dubu 230 a kasashe da dama na nahiyar Asiya. Akalla kasa ta motsa har sau 40 a cikin kwanaki biyu da suka wuce.