1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan Tsattsan Baki A Jamus

June 7, 2006

Sabuwar kididdiga ta nuna cewar mutane miliyan 15.3 ne ke da salsala daga ketare a Jamus

https://p.dw.com/p/Btzq

Kawo yanzun dai ma’aikatar kididdiga ta Jamus ta sikankance cewar yawan bakin dake zaune a kasar bai zarce miliyan bakwai ba, wanda ya kama kwatankwacin kashi 10% na illahirin al’umar kasar. Amma a yanzun an gano cewar wannan kididdiga na tattare da kurakurai, domin kuwa wani binciken da masana kimiyya suka gudanar sun gano cewar yawan masu toshe daga ketare a kasar ta Jamus ya kai miliyan 15 da dubu 300. Hakan na ma’ana ke nan cewar kimanin kashi daya bisa biyar na illahirin mazauna Jamus na da nasaba da hijira. Bisa ga ra’ayin Johann Hahlen, shugaban ma’aikatar da kiddidiga ta Jamus, wadannan bayanai na masu yin nuni ne da gaskiyar cewar Jamus, tun fil-azal kasa ce da ta saba karbar ‘yan gudun hijira.

“Idan kana da al’uma da kashi 19 cikin dari daga cikinsu na da salsala daga ketare, ana iya batu a game da wata al’uma mai tasirin ‘yan gudun hijira.”

Wannan sabuwar kididdigar da aka bayar ta zo ne sakamakon sauyin da aka samu ga salon kidayar jama’a. Domin kuwa a zamanin baya idan an yi batu a game da baki, ana nufin wadanda ba su da takardun fasfo na Jamus. Amma a sabuwar salon na kidayar jama’a ana hadawa ne da dukkan mutanen dake da salsala daga ketare. Wato wadanda ko dai su kansu ne suka yi kaura zuwa Jamus, ko iyayensu ko kuma kakanninsu. Ga dai abin da Johann Halen yake cewa:

“Daga cikin wadannan mutane miliyan 15 da dubu 300 akwai mutane miliyan goma da suka yiwo hijira zuwa nan kasar da kansu. Wannan bangaren ya kunshi mutane miliyan biyar da dubu 600 da suka shigo kasar suka kuma ci gaba da zama a matsayin baki, sai kuma wasu miliyan uku da suka rikide zuwa Jamusawa. Sai kuma tsattsan Jamusawa miliyan daya da dubu dari takwas da suka yiwo kaura a baya-bayan nan daga gabacin Turai.”

Sabuwar kididdigar ta bayyanar a fili cewar Jamus na bukatar ‘yan gudun hijira da zasu yi kaka-gida a cikinta saboda suna taimakawa wajen sabunta al’amuran kasar. Domin kuwa galibi wadannan ‘yan gudun hijira su kan hayayyafa da yawa fiye da takwarorinsu Jamusawa. To sai dai kuma a inda take kasa tana dabo shi ne akasarin tsattsan ‘yan gudun hijirar su kan saje da takwarorinsu Jamusawa su canza salon rayuwarsu suna masu rage yawan haifuwa. To dama masu iya magana su kan ce zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin gashi.