1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan 'yan gudun hijira da ke shigowa Jamus ya ragu

Mohammad Nasiru AwalApril 25, 2016

Sanya Aljeriya da Marokko da Tunisiya a jerin kasashe masu kwanciyar hankali ya rage yawan 'yan gudun hijirar kasashen da ke shigowa Jamus.

https://p.dw.com/p/1IcOe
Flüchtlinge aus Nordafrika
Hoto: picture-alliance/dpa

Wani rahoto da jaridun wata kungiyar 'yan jarida mai suna Funke suka buga a wannan Litinin ya nuna cewa yawan 'yan gudun hijira da ke shigowa tarayyar Jamus daga kasashen Aljeriya da Marokko da kuma Tunisiya ya ragu matuka idan aka kwatanta da shekarar 2015. Rahoton wanda ya danganta alkalummansa da wani rahoton da ofishin kula da batutuwan da suka shafi kaura da 'yan gudun hijira na tarayyar Jamus ya tura wa majalisar dokoki, ya ce yawan 'yan gudun hijira ya matukar ja da baya ne sakamakon matakin da Jamus ta dauka na sanya sunayen kasashen uku a jerin kasashen da ke da zama lafiya kuma suka kasance tudun mun tsira. Hakan na nufin ke nan cikin sauki, ana iya mayar da 'yan gudun hijira daga wadannan kasashe.