1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yiwuwar Shigar Da Sojojin Jamus A Ayyukan Kiyaye Zaman Lafiya A Afurka

August 27, 2004

Bisa ga ra'ayin ministan tsaron Jamus Peter Struck kamata yayi kasar ta fara tunanin shigar da sojojinta a ayyukan kiyaye zaman lafiya a nahiyar Afurka.

https://p.dw.com/p/Bvgz
Ministan Tsaron Jamus Peter Struck
Ministan Tsaron Jamus Peter StruckHoto: AP

A cikin wata hira da aka yi da shi ta gidan rediyo a jiya alhamis ministan tsaron Jamus Peter Struck yayi nuni da cewar wajibi ne sojan kasar su samu cikakken horo na musamman, wanda zai ba su damar shiga a rika damawa da su a ayyukan kiyaye zaman lafiya da kwantar da tarzoma a nahiyar Afurka. A halin yanzu haka sojojin Jamus 290 ne ke gudanar da aikinsu a yankin tekun bahar-maliya a karkashin matakan yaki da ta’addanci na kasa da kasa a karkashin jagorancin kasar Amurka. Kazalika akwai wasu hafsoshin sojan Jamus dake rufa wa matakan sa ido akan yarjejeniyar zaman lafiyar Habasha da Eritrea. Ko da yake an sha gabatar da kiraye-kirayen tura sojojin Jamus zuwa sauran sassan da ake fama da rikici a cikinsu a nahiyar Afurka, amma kawo yanzu gwamnati a fadar mulki ta Berlin ta ki yarda da ta tura wata kakkarfar rundunar mayaka zuwa nahiyar bisa dalilin cewar tana da dimbim sojoji a Afghanistan kuma a saboda haka ba zata iya daukar wani karin nauyi kanta ba. Amma fa a cikin hirar da aka yi da shi ta gidan rediyo a jiya alhamis, ministan tsaro Peter Struck ya fito fili yana mai bayanin cewar Jamus ba zata iya fakewa da irin wannan hujja ba muddin tana sha’awar samun wata dawwamammiyar kujera a kwamitin sulhu na MDD. Kazalika wajibi ne ta ba da la’akari da irin alhakin da ya rataya wuyanta dangane da makomar nahiyar Afurka, musamman a matsayinta na tsofuwar ‚yar mulkin mallaka. Peter Struck ya kara da cewar:

A hakika ba zan iya cewar ba mu da ikon tura karin sojoji domin aikin kiyaye zaman lafiya a kasashen ketare ba, ta la’akari da gaskiyar cewa rundunar sojanmu ta kunshi dakaru dubu 270, wadanda duka-duka dubu takwas ne kacal daga cikinsu ke aikin kiyaye zaman lafiya a ketare.

Peter Stuck na samun cikakken goyan baya akan wannan manufa daga ministan harkokin waje Joschka Fischer wanda ya fito fili yana kalubalantar masu ikirarin cewar rikicin Afurka bai shafi bukatun Jamus ba. Fischer yayi gargadi a game da cewar rikice-rikicen dake addabar Afurka ka iya yin tasiri tare da gurgunta tsaro a nahiyar Turai. A saboda haka ya zama wajibi Jamus da sauran kawayenta na nahiyar Turai su yi hadin kai domin taimaka wa Afurka wajen warware rikice-rikicen dake addabar kasashenta. Bugu da kari ma dai yawa-yawancin wadannan rikice-rikice sun samu tushensu ne daga zamanin mulkin mallakan Turawa a nahiyar ta Afurka. To sai dai kuma kungiyoyin taimako masu zaman kansu na kyamar ganin Jamus ta shigar da sojojinta domin aikin kiyaye zaman lafiya. Bisa ga ra’ayinsu abu mafi alheri shi ne matakai na riga kafin rikici, wanda ke ma’anar bunkasa yawan taimakon raya kasa domin tayar da komadar tattalin arzikin kasashen nahiyar, saboda galibi rikice-rikicen suna da nasaba ne da matsaloli na tattalin arziki.