1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yobe ta karyata kanta kan 'yan matan Dapchi

Mouhamadou Awal Balarabe
February 22, 2018

Gwamantin jihar Yobe da ke yankin Arewa maso gbashin Najeriya ta yi amai ta lashe game da batun ceto 'yan matan makarantar garin Dapchi da ake zargin 'yan Boko Haram da sacesu.

https://p.dw.com/p/2tAWj
Karte Nigeria Dapchi ENG

Gwamnatin jihar Yobe ta fito fili ta bayyana wa 'iyayen 'yan matan makarantar sekandaren garin Dapchi da aka sace cewar ba a kubutar da su ba.  Kakakin gwamnan jihar Yobe Abdullahi Bego ya yi ta bada labarai da ke cin karo da juna tun bayan da 'Yan Boko Haram suka yi awon gaba da su, inda ya fara karyata labarin kafin daga bisani ya ce an sakesu, sannan ya lashe amansa.

Cikin hirar da suka yi da kanfanin dillacin labaran Jamus DPA, iyayen 'yan matan suka ce sun gana da gwamnan Ibrahim Geidam wanda ya tabbatar musu cewa ba a ji duriyar 'ya'yansu ba tun bayan da aka sacesu. Sai dai ya ce sojoji na ci gaba da farautar mayakan Boko Haram da ake zargi da sace daliban, bayan da suka kai hari a makarantarsu a ranar Litinin.

An kiyasta cewar 'yan mata 101 ne 'yan bidiga suka sace a Dapchi, shekaru uku bayan sace 'yan mata kusa 200 a garin Chibok na jihar Borno, lamarin da ya tada hankulan kasashen duniya.