1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin Kamaru da Jamus

April 1, 2010

Hukumomin kamaru da kuma takwarorinsu na Jamus sun kammala zaman waiwayen daɗɗaɗiyar dangantakar da ke tsakaninsu a fanninnin kiwon lafiya, alƙinta muhalli da kuma fasaha.

https://p.dw.com/p/MjKk
Jakadiyar Jamus da ministan raya ƙasa na kamaruHoto: Pressestelle deutsche Botschaft Yaoundé

Ra´ayin wakilan fadojin mulki na Berlin da kuma na Yaounde ya zo ɗaya game da yadda sassa biyu ke aiwatar da manufofin raya ƙasa da suka cimma tsakaninsu tun shekaru da dama da suka gabata. Hasali ma dai, tawagar ta Jamus ta yaba da yadda aka samu ci gaba mai ɗorewa a fannonin sakar ma ƙananan hukumomi mara, da kuma wadata mazauna karkara da abubuwan more rayuwa. yayin da a ɗaya hannu, jami´an Kamaru suka yaba da irin ruɓanya tallafin na tsabar kudi da kuma fasaha da tsohuwar uwar gijiyartasu ke samar ma ƙasar. Biliyon 12 na CFA da gwamantin ta Jamus ta kashe domin wadata kauyuka 45 da rijiyoyin burtsatsai na daga cikin abubuwan da yayan na kamaru ke ci gaba da alfahari da shi a dangantakar ƙasashen biyu.

Mata na daga cikin waɗanda suka fi cin gajiyar tallafi na Jamus a kamaru, domin kuwa hukumar fasaha ta wannan ƙasa, wato GTZ ta girka wani shiri na yanke talauci ga matan. Hakazalika ta naƙaltar da su hanyoyin da za su bi domin yakar abin da ya daɗe yana ci musu tuwo a ƙwarya: wato mayar da su saniyar ware da aka yi ta yi abaya a gudanar da harkokin mulki. Hajiya Salamatu Mai Akwai ɗaya daga cikin shugabannin mata na Kamaru, ta ce a yanzu kan mage ya waye.

Kamerun Bantu-Kinder
Jamus na neman kyautata rayuwar yara manyan gobeHoto: Carine Debrabandère

Kiwon lafiya ma ba a barshi a baya ba, a inda tarayyar ta Jamus ta haɗa guywa da gwamanatin kamaru wajen samar wa masu fama da cutar AIDS ko SIDA nau´o´in magagunguna masu rage raɗaɗin cutar. Hakazalika a ko wace shekara, kwararrun likitocin Jamus na niƙa gari i zuwa arewacin Kamaru domin ɗinke bakin yara ƙanana da ke fama da cutar ƙabba. Lamarin da iyaye suka yabawa ainin.

Babban abin da Jamus ke ci gaba da alfahari da shi a halin yanzu a kamaru dai, shi ne ci gaba da kasancewa ƙasar Afrika da 'yayanta suka runguma, tare da naƙaltar harshen jamusanci. karin Elsa Blumberger-Sauerteig da ke zama jakadiyar jamus a Kamaru ta yi tsokaci tana mai cewa

"Ta ce a kamaru kusan mutane dubu 200 ne ke karantar jamusanci a makarantu. sa´annan kuma da akwai ƙwararrun malaman kamaru dubu da ke karantar da harshen. yayin da a Jamus kuma muke da ɗalibai Kamaru dubu 6, dake karantar jamusanci da kimiyyar hallitu da sauransu."

Holzfäller bei der SEFAC im Südosten von Kamerun
Wajibcin kamaru na alƙinta dajin da Allah ya hore mataHoto: DW / Debrabandère

sai dai ci gaba da rikon sakainar kashi na albarkatun daji da Allah ya hore ma kamaru ne, ya ke kawo ruɗu a sauye-sauye da suka cimma. Amma sassa biyu sun ƙudiri aniyar amfani da zaman da za su yi a nan birnin Bonn a watan satumba mai zuwa wajen shata sabon babin dangantarka tsakanin kamaru da kuma Jamus. Ita dai Kamaru, ita ce ƙasa ta uku baya ga Afghanistan da kuma Kwango Demokaradiya da ta fi samun tallafi Jamus a duniya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar