1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin dasa bam a taron G8

June 24, 2010

Gwamnatin Kanada ta ce ta bankaɗo shirin ƙaddamar da hari a lokacin taron G8 da kuma na G20

https://p.dw.com/p/O2Y9
Hoto: picture-alliance/dpa

Dabbannin 'yan Sanda ne hukumomin ƙasar Kanada suka tura domin zama cikin shirin ko ta kwana, bayan da gwamnatin ƙasar ta sanar da bankaɗo wani yunƙurin tada bam a lokacin tarukan ƙungiyar ƙasashe 8 masu ƙarfin tattalin arziƙi, da kuma na ƙungiyar ƙasashe 20 - masu ƙarfin tattalin arziƙi ta G20, waɗanda birnin Toronto na ƙasar ta Kanada zai karɓi baƙunci. Jami'an 'Yan Sanda suka ce suna tuhumar wani haifaffen birnin Toronto - mai shekaru 37 da haihuwa, da kuma matarsa da laifin mallakar sanadaren da ka iya tarwatsewa.

A jiya Laraba ce dai, 'yan sandan suka gano wannan shirin. Tsarewar kuma ta zo ne a dai dai lokacin da shugabannin ƙasashen duniya suka fara isa birnin Toronton Kanadar, domin yin musayar yawu game da farfaɗowar tattalin arziƙin duniya da kuma bunƙasar ƙasashen duniya. In anjima kaɗan ne shugabannin ke fara taron ƙungiyar G8 a yankin Huntsville dake arewacin birnin na Toronto. Da yammacin gobe jumma'a ne kuma - idan Allah ya kaimu ƙungiyar ƙasashe 20 dake da ƙarfin masana'antu a duniya ke fara nasu taron.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Muhammad Abubakar