1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin girka sabuwar gwamnati a Somalia

August 8, 2006
https://p.dw.com/p/BunO

Praministan ƙasar Somalia, Ali Mohamed Gedi, ya gana yau da shugabanin ƙungiyoyi daban daban na ƙasa, domin tantanawa,a kan matakan girka sabuwar gwamnatin riƙwan ƙwarya, a sakamakon marabus babu ƙaƙƙabtawa, da wasu ministocin gwamnati su ka yi, a kwanakin da su ka gabata.

Ranar jiya , shugaban ƙasa Abdullahi Yusuf Ahmed, ya sanar da yunƙurin girka sabuwar gwamnatin , a makon da mu ke ciki.

Ya kuma ce, an samu bakin zaren warware rashin fahintar da ta hadasa, murabis ɗin ministocin.

Idan dai ba a mata ba, a tsukun mako guda, ministoci 43 su ka bar muƙamman su, domin nuna adawa ga sallon mulkin praminsita, mussamman a game da taurin kan da ya nuna, na ƙin tantanawa da dakarun kotunan islama, da kuma izinin da ya ba ƙasar Ethiopia, na ta girke dakaru a Somalia.

Saidai masu sharhi a kan harakokin siyasar Somalia, sun hango cewar, wannan cenjin gwamnati ba zai kawo ƙarshen rikicin ƙasar ba, muddun babu dakarun kotunan islama a ciki, wanda a halin yanzu ke riƙe da Mogadiscio babban birni, da ma wasu sauran yankuna na ƙasa.