1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin inganta tsaro a Afghanistan

August 17, 2010

Shugaban Afghanistan ya rusa kanfanonin tsaro masu zaman kansu na ƙasar

https://p.dw.com/p/OpjD
Shugaba Hamid KarzaiHoto: PA/dpa

Shugaba Hamid Karzai na Afghnaistan ya haramta ma kanfanonin masu zaman kansu na ketare gudanar da ayyukan tsaro a ƙasarsa. Wata doka da ya rattaba hannu a kanta a wannan talata ya ɗibar musu wa'adin wata hudu domin kawo ƙarshen ayyukan da suka gudanarwa, tare da ficewa daga ƙasar ta Afghnistan.

Wannan doka ba za ta shafi kanfanonin da ke kula da ofisoshin jakadan ƙasashen waje da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa ba. Waɗannan kanfanoni da ke samar wa mutane150 000 aiki, sun yi ƙaurin suna wajen safarar makamai, tare da aikata ayyukan assha a ƙasar.

Masharhanta sun danganta wannan mataki na Hamid Karzai da yunƙurin da ya fara na mayar da harkar tsaron ƙaraƙashin kulawar rundunar tsaron ƙasar.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar