1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin juyin mulki a Nijar

October 16, 2010

Mahukunta a Nijar sun tsare wasu hafsoshin soji, waɗanda ake tuhuma da yunƙrin hamɓare gwamnati.

https://p.dw.com/p/PflO
Dogarawan shugaban mulkin sojin NijarHoto: AP

A jamhuriyar Nijar rohotanni suka ce an tsare mutum na biyu mafi girman muƙami a gwamnatin sojan ƙasar kanal Abdullaye Badie. Kanal Badie wanda a makwanan gwamnatin soji ta rusa muƙamin ofishin da yake riƙe da shi, tun lokacin makomarsa ta shiga ƙila waƙala. A jiya dai shugaban ƙasar Nijar Janar Salihu Jibo ya shaidawa wakilin ƙungiyar ECOWAS cewa, babu wanda aka tsare. Wata majiyar tsaro ta ce an san tabbas Kanal Badie da kuma Leftenen kanal Abdou Sadiko suna tsare, inda ake yi musu binciken ƙoƙarin hamɓare gwamnati dama shirya makircin hallaka shugaba mai ci Janar Salihu Jibo. Majiyar ta ce tun watanni uku da suka gabata, aka sa ido kan waɗanda ake zargin, har sai yanzu da dubunsu ta cika. A dai yi ta yaɗa raɗe-raɗin yunƙurin juyin mulki, amma sojojin ƙasar suka yi gom da bakinsu. Ko ba komai dai an ƙarfafa matakan tsaro a birnin Yamai, musamman idan gari ya fara duhu. Rohotanni dai na cewa an tsare sojojin a ofishin jandarma dake birnin Yamai.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammad Nasir Awal