1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin juyin mulki a Tchad

March 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4y

Gwamnatin ƙasar Tchadi ta bada sanarwar murƙushe wani yunƙurin juyin mulki a daren jiya talata.

Ministan watsa labarai Hurmadji Moussa Doumgor ya sanar da gidan Redion France cewa, a halin yanzu an capke 2, daga manyan jami´an sojan kasa, da aka tabbatar su na da hannu a cikin wannan maƙarƙashiya ta kiffar da shugaba Idriss Deby.

Gungun yan tawayen SCUD, na ƙasar Tchad, ya tseguntawa kamapanin dullacin labarum Reuters, cewar, ko shakka babu, shi ke da alhakin shirya wannan juyin mulki, to amma, ya fasa, bayan da wasu jannarori masu biyyaya ga gwamnmati, su ka ci amana ta hanyar tona assirin maƙarƙashiyar.

Kakakin na gwamnati, ya ce tunni, dakaru sun shiga farautar yan ƙungiyar CSUD ,da ta ƙunshi sojojin da su ka arce bara, daga rundunonin soja, domin kafa ƙungiyar tawaye, da a halin yanzu ta girka sansani a iyaka da ƙasar Sudan.

So tari Shugaba Idrissd Deby, ya sha zargin hukumomin Sudan da kunna wutar rikicin tawaye a ƙasar Tchad.

A yammancin yau, opishin ministan harakokin wajen France, ya hiddo sanarwa, wada a cikin ta ya bayana cewar ya na bi sau da ƙafa, halin da ake ciki a ƙasar Tchad.

A halin da ake ciki, babu shiga babu fita, a wannan ƙasa, kuma an katse dukan wayoyin talho, da ƙasashen ƙetare.