1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin kai hari a Turai

September 29, 2010

An murƙushe wani yunƙurin kai hari a wasu ƙasashen Turai.

https://p.dw.com/p/PPRJ
Hasumiyar Eiffel Tower na Faransa.Hoto: AP

Rahotanni daga Birtaniya sun yi nuni da cewa hukumomin leƙen asiri sun murƙushe wani yunƙurin kai hare-hare a nan Jamus da Faransa da kuma Birtaniya. Gidan telebijan Sky News na ƙasar Birtaniya ya ce wasu majiyoyi da ke da nasaba da aikin leƙen asiri sun ce daga Pakistan ne aka kyankyashe wannan shiri. Ya ƙara da cewa a birnin London da wasu birane da ke nan Jamus da Faransa ne aka shirya kai hare-haren. An gano wannan shirin ne sakamakon musayar labarai da aka yi tsakanin ƙasashen uku da Amirka. A jiya Talata sai da mutane suka ƙaura daga ginin Eifell Tower na ƙasar Faransa sakamakon kashedin da aka yi game da yiwuwar fuskantar hari a wannan wuri. Karo na biyu kenan da aka ƙaura daga wani ginin tarihi a wannan wata.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu