1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

140710 Afrika Klimawandel Initiative

July 15, 2010

An ƙaddamar da wani shirin haɗin gwiwa tsakanin Jamus da ƙasashen Afirka 15 domin yaƙi da ɗumamar yanayi da gurgusawar hamada a nahiyar Afirka

https://p.dw.com/p/OJhf
Yaƙi da ɗumamar yanayi da gurgusawar hamada a Afirka

Gwamnatin Tarayyar Jamus, tare da haɗin gwiwar wasu ƙasashen Afirka 15 sun yanke shawarar girka cibiyoyin bincike guda biyu game da ɗumamar yanayi. A birnin Berlin na nan Jamus aka ƙaddamar da wannan shiri.

A shekaru masu zuwa fiye da duk sauran sassa na duniya, Afirka za ta yi fama da matsalar ɗumamar yanayi, sannan saɓanin sauran ƙasashen duniya, nahiyar Afirka ba ta da isassun kayan aiki da husa´o´in fuskantar wannan ƙalubale.

Ministar horo ta Jamus Annette Schavan ta yi ƙarin haske game da burin da gwamnatin Tarayya ke buƙatar cimma ta fuskar gina cibiyoyin binciken ta ce:

"Ba wai kawai mun ƙaddamar da wannan shiri ne ba da fatar baka. A Afirka za mu girka cibiyoyin binciken har guda biyu, ɗaya a kudu ta biyun kuma a yankin yammancin nahiyar. Za mu yi aiki kafaɗa da kafaɗa tare, ´yan siyasa su yi nasu aiki, su ma ƙwarrarun masana su yi nasu."

Manyan husa´o´i da za a ƙadamar a wannan tsari, sun haɗa da koyarwa Afirka yadda za ta iya gudanar da harakokin noma irin na zamani, misali dubarun ban ruwa ko amfani da taki, da gyara gona da dai sauran dubaru.

Sherry Ayittey itace ministar horo da muhhali a ƙasar Ghana, ta bayyana matsayin Afirka game da batun ɗumamar yanayi da gurgusawar hamada:

"A ƙasashen yammacin Afirka duk matsalr iri guda ce tun daga Guinea Bisau har zuwa Kamaru. Mu na da kurmi wanda ke cikin barazanar bacewa saboda saran itatuwa barkatai, sai kuma reren Sahara wanda har kulum sai kara gurgusawa ya ke daga arewa zuwa kudu.Sannan mu na fama da karanci ruwa da wutar lantarki."

Ɗaya daga mahimman aiyukan wannan cibiyoyin nazarin ɗumamar yanayi da za a kafawa shine tattaro bayanai masu nasaba da batun a tsawan shekarun da suka gabata.Wannan cibiya za ta aiki tare da haɗin gwiwa da jami´o´i da kuma masana ta fannin yanayi.Norbet Jürgens masani ne ta fannin kimiyar tsirrai a jami´ar Hamburg kuma shi za shi jagorancin cibiyar a yankin kudancin Afirka, ya bayyana mahimmanci haɗa gwiwa da Afirka a cikin wannan bincike:

"Wannan shine karon farko da za a ƙaddamar da aiki cikin haɗin gwiwa na zahiri tare da Afirka. Don cimma burin da mu ka sa gaba cilas mu yi tsari mai kyau kamin fara gudanar da binciken, kuma cilas mu tara bayyanan binciken da aka gudanar a shekarun baya".

Wani mataki mai karfi a cikin wannan shiri shine horrar da ´yan Afrika game da kimiyar yanayi, saboda haka Jamus za ta gina makarantu bakwai a yankin yammancin Afirka, inda za a koyi ilimi mai zurfi ta fannin kimiyar yanayi.

A jimilce a cikin shekaru biyu masu zuwa, ofishin ministan Jamus mai kula da bada horo zai zuba tsabar kuɗi Euro miliyan biyar a cikin wannan tsari. Idan kuma cibiyoyin suka fara aiki gadan-gadan yawan kuɗin da Jamus za ta kashe zai tashi Euro miliyan 100.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Mohammad Nasiru Awal