1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin 'yanto wani Bafaranse a Mali

July 24, 2010

Faransa na ƙoƙarin ƙara matsa ƙaimi domin belin ɗan ƙasar ta

https://p.dw.com/p/OTjZ
Sojojin ƙasar Faransa a Mali

Ƙasar Faransa na ƙoƙarin ƙara matsa ƙaimi domin yin belin wani ɗan ƙasar ta da reshen ƙungiyar Alƙaida na Aqmi ya ke yin garkuwa da shi a ƙasar Mali.

Mutuman mai sunan Michel Germaneau da aka sace a Niger a cikin watan Afrilu ɗan shekaru 78 na gudanar da ayyukan agaji ne a ƙasar Mali.

Wasu rahotannin da ba a tabbatar da gaskiyarsu ba, sun ce yanzu haka ana can ana ci-gaba da yin ɗauki ba daɗi tsakanin 'yan ta'addar da kuma wasu sojojin ƙawance na ƙasashen yankin Hamada da ke samun goyon bayan ƙasashen Faransa da Amurka.

A wani farmakin dai da sojojin ƙasar Moritaniya suka kai a ranar Alhamis da ta gabata kan 'yan ƙungiyar na Aqmi, sun kashe mutane shidda kana kuma suka raunata wasu daga cikin 'yan ƙungiyar da suka samu arcewa.

Mawallafi: Abdurrahmane Hassane

Edita: Mohammad Nasiru Awal