1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kawo karshen rikicin Yemen

Lateefa Mustapha Ja'afarMay 2, 2016

Babban jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Yemen Ismail Ould Cheikh Ahmed ya ce wakilan gwamnatin kasar, sun dakatar da zama kan teburin sulhu domin kawo karshen rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/1Igm9
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Yemen Ismail Ould Cheikh Ahmed
Hoto: Getty Images/AFP/Y.Al-Zayyat

Ahmed ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce bangaren gwamnatin ya janye daga tattaunawar share fage da ke gudana a kasar Kuwait sakamakon abin da suka bayyana da cewa 'yan tawayen kasar sun kai wani sabon hari a birnin Amran na Yemen din, sai dai ya ce duka bangarorin biyu sun yi alkwarin bayar da hadin kai da kuma tabbatar da ganin sun shawo kan banbance-banbancen da ke tsakaninsu domin ganin an shawo kan rikicin kasar da ya lashe rayuka masu yawa, idan aka dawo zauren tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniyar ke jagoranta. Rikici dai ya barke tsakanin gwamnatin kasar ta Yemen da ke samun goyon bayan dakarun rundunar taron dangi da Saudiya ke wa jagoranci da kuma 'yan tawayen Houthi da suka kwace iko da Sanaa babban birnin kasar a watan Satumba na shekara ta 2014.