1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin bunkasa harkokin kiwo a nahiyar Afirka

February 27, 2017

Wakilai na kungiyoyi masu fafutuka na Afirka na gudanar da wani taro a Nijar da nufin bunkasa saha'anin kiwo.

https://p.dw.com/p/2YJpa
Angus-Rinder auf einem Demeter-Bauernhof
Hoto: picture-alliance/Presse-Bild-Poss

A Jamhuriyar Nijer wasu shugabannin kungiyoyin makiyaya da na mazauna karkara ne daga  wasu kasashe na yammacin Afirka ke halartar wani taro don duba batun matsalolin da makiyaya da ma mazauna karkara ke fuskanta a wannan lokacin na rani.

Batutuwan tsaro,na shige da ficen makiyaya da na mazauna karkara tsakanin kasashen yammacin Afirka uwa uba da rashin ingantaciyyar ciyawar dabbobi na daga cikin batutuwan da suka mamaye taron wanda shi ne irinsa karo na farko da ake yi a Nijar.Kimanin gibin tan miliyan 12 na ciyawar dabbobi ne dai gwamnatin ta Nijar ta ambaci ta ke bukata a wannan shekarar don tinkarar matsalolin na kiyo.A farkon watan gobe ne dai kungiyoyin suka ayyana da cewar za su gamu a birnin Abuja na tarayyar Najeriya don ci gaba da tattauna wannan batu.