1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin kasashen kudancin Afrika na shawo kan Mugabe

Hauwa Abubakar AjejeMarch 28, 2007

Shugabannin kasashen kudancin Afrika sun hallara a kasar Tanzania domin duba halinda ake ciki a kasar Zimbabwe yayinda yan sanda suka sake tsare shugaban adawa Morgan Tsvangrai na yan saoi kadan kafin sake shi.

https://p.dw.com/p/Btvv
Robert Mugabe
Robert MugabeHoto: AP

Shugaba Jikaya Kikwete na kasar Tanzani yayi kiran wannan taro na gaggawa sakamakon rudani da kuma kira da kasashen duniya sukeyi game da halinda ake ciki a kasar ta Zimbabwe.

Majiyoyi daga jamiyar MDC sun baiyana cewa an tsare Tsvangrai tare da wasu magoya bayansa 20 cikin wani samame da yan sanda suka kai hedkwatar jamiyar MDC a birnin Harare.

Yayinda kuma kasashen yammacin duniya suka fito fili suna masu suka da yin Allah wadai ga shugaba Robert Mugabe,kasashen yammacin Afrika sunyi taka tsantsan a cikin kalamansu game da wannan batu,duk kuwa da cewa sune zasu fi yin hasara idan rikici ya barke a kasar ta Zimbabwe.

A hira da DW Morgan tsvangari ya nuna rashin jin dadinsa ganin cewa kasashen na kudancin Afrika basu yi Allah wadai da abinda Mugabe yakeyiwa abokan adawarsa.

``A gaskiya mun zaci zasu yi Allah wadai da kakausar murya fiye da haka,maimakon shiru da wasu sukayi,kodayake muna yabawa sauran kasashen afrika da suka fito fili sukayi magana kann wannan batu da kuma bada shawarar abinda ya kamata a yi a zimbabwe.``

Jamian kasar Tanzania dai sunce shugabannin na kungiyar kasashen kudancin Afrika suna kokarin ganin sun janyo hankalin Mugabe dake ci gaba da nuna taurin kai daya tattauna da shugabanin jamiyar MDC tare da nufin kawo karshen wannan rikici dake neman tarwatsa kasar ta Zimbabwe.

Morgan Tsvangari yace jamiyarsa a shirye take ta tatauna da gwamnati,sai dai gwamnatin ce bata shirya ba.

``Sai dai rashin amincewa na tattaunawar ba daga garemu bane,daga jamiyar Zanu PF ne,amma har yanzu muna kira ga yan zimbabwe masu kishin kasa da su duba hanyoyin ceto kasar,su hada kai wajen tsara makomar kasar“

Duk da cewa jamaa da dama na ganin kasashen kudancin Afrikan ba zasu yi Allah wadai da Mugabe ba amma wani tsohon na hannun daman Mugabe ya fadawa wata jarida ta Burtaniya cewa shugabbanin na kudancin Afrika zasu nunawa Mugabe cewa yana neman ya kawo koma baya ne ga dukkanin kudancin Afrika kuma dole ne ya sauka idan waadin mulkinsa ya kare a shekara mai zuwa.

Tunda da farko Mugabe wanda yake halartar wannan taro,ya alkawartawa kungiyar ta SADC cewa zai sauka da zarra waadin mulkinsa ya kare a 2008.

Sai dai kuma ya canza raayi game da hakan inda tuni jamiyarsa ta ZANU ta shirya wani taro a yau don sake bashi damar ci gaba da mulki har zuwa 2010 amma ta soke taron sai an kammala babban taron kungiyar ta SADC.

Baya ga tashe tashen hankula na siyasa a Zimbabwe,hauhauwan farashin kayayiyaki da suka nunka ribi 1,730 da rashin aikin yi da ya kai kashi 80 cikin dari sun tilasatawa yan kasar kusan miliyan 3 yin hijira wanda kuma hakan ya janyo tabarbarewar harkokin kasuwanci a yankin.