1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin shigar Turkiya Ƙungiyar tarayyar Turai

December 14, 2006
https://p.dw.com/p/BuY2

Shugaban hukumar tarayyar Turai Jose Manuel Barrroso ya yi kashedin cewa shawarwarin shigar Turkiya ƙungiyar tarayyar Turai ka iya ɗaukar tsawon shekaru kimanin goma sha biyar. A hirar da ya yi da wata mujalla Die Welt ta nan Jamus, Barroso ya kuma ja hankali ga dogon burin da ake dorawa ga ƙasar Jamus wadda zata ƙarbi shugabancin ƙungiyar tarayyar Turan a cikin watan Janairu na shekara ta 2007. Yace bai kamata a ɗora buri ga Jamus ta warware dukkan matsalolin ƙungiyar tarayyar turai ba.