1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin tsige shugaba Jacob Zuma

Ramatu Garba Baba
August 8, 2017

A wannan Talatar majalisar dokoki a kasar Afrika ta Kudu ke shirin kada kuri'a yanke kauna akan shugaba Jacob Zuma, al'amarin da ka iya tilasta masa sauka daga mukaminsa.

https://p.dw.com/p/2htKC
Misstrauensvotum Südafrika
Hoto: Reuters/M. Hutchings

A wannan Talatar majalisar dokoki a kasar Afrika ta Kudu ke shirin kada kuri'ar yanke kauna kan shugaba Jacob Zuma, al'amarin da ka iya tilasta masa sauka daga mukaminsa. Gwamnatin shugaba Zuma ta fuskanci koma baya bisa zarge-zargen rashawa da ta dabaibaye mulkinsa. Akalla sau shida 'yan majalisa suka yi kokarin tsige shi daga karaga amma ba tare da yin nasara ba, sai dai wannan shi ne karon farko da ake shirin kada kuri'ar cikin sirri kamar yadda bangaren adawa ya bukata da kuma ya sami amincewar kakakin Majalisar Baleka Mbete a jiya Litinin.

A wajen ginin majalisar da ke birnin Cape Town kuwa an sami gamayar masu zanga zangar na masu goyon baya da kuma adawa da shugaban. Idan har bukatar 'yan adawa da shugaba Zuma ta yi nasara a majalisar, hakan zai tilasta masa da mukarrabansa yin murabus, inda kakakin majalisar za ta zama shugaban kasa ta riko na tsawon wata guda kafin zaben sabon shugaban kasa.