1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunwa a Somalia

Zainab A MohammadSeptember 15, 2005

Majalisar dunkin duniya ta koka dangagane da kuncin rayuwa a tsakanin alummomin Somalia

https://p.dw.com/p/BvZc
Hoto: AP

Kimanin mutane million guda ,wadanda suka hadar da fararen hula da suka rasa matsugunnensu ne ke fama da matsalar yunwa a kasar Somalia,wadda ta fuskanci rigingimun kabilanci na tsawon shekaru 14,inji rahotan mdd.

A rahotanta na baya bayan data kan fitar kowane wata a kan kasar ta Somalia,majalisar dunkin duniya ta sanar dacewa kusan mutane million daya ner ke fama da matsalar yunwa wadanda kuma suka hadar da mutane dubu 370 dake bukatar agajin abinci na gaggawa,wadanda kuma dole ne a sanyasu cikin agajin samara da abinci na gaggawa a shekara ta 2006.

Daga cikin wannan adadin inji majalisar kimanin dubu 345 na fuskantar matsaloli na rayuwa,a yayinda wasu dubu 197,ke neman agajin rayuwa na gaggawa.

Rahotan yayi nuni dacewa zaafi mayar da hankali kan tallafawa mutane kimanin dubu 169 dake cikin kuncin rayuwa a tsibirin juba wanda ke kudancin somaliya.

Tun a watan mayu nedai wata hukuma dake kula da matsalolin fari ta Amurka tayi gargadin cewa jinkiri da a ka samu ta fanning ruwan sama zai addabi yankunan kudanci,inda nan ne kashi 50 daga cikin dari na abincin kasar ke fitowa.

Bugu da kari rahotan yace an samu kashi 43 daga cikin 100 na dala million 164 da gidauniyar neman taimako ta kaddamar ,idan aka kwatanta da kashi 27 daga cikin 100 na wanda aka samu bara.

Kasar dake da mutanen da yawansu yakai million 10,Somalia ta kasance ba tare da gwamnati ba,tun bayan hambare mulkin Dan kama karya Mohammed Siad Barre a shekara ta 1991,inda kasar ta fuskanci fadace fadace na hauloli dake adawan neman ragamar mulki.

Jamian agaji na cigaba da fuskantar cikas wajen gabatar da kayyayakin taimako saboda matsalolin hare hare da ake afka musu da ita.

Yanzu haka dai gwamnatin rikon kwarya na Somalian dake gudun hijira a kasar Kenya tun bara,ta komo gida tun a watan yuni,inda take da matsuguni na wucin gadi a garin Jowhar,adangane da matsaloli na rashin tsaro da birnin Mogadisho ke ciki.

A hannu guda kuma an gano wani babban jirgin rowan mdd dake dauke da agajin abinci wa wadanda balain tsunami ya ritsa dasu ,inda yanzu jirgin ya doshi tashar jirgin ruwa dake El-Maan,arewacin Mogadisho.To sai dai babu tabbaci ko jirgin ruwan da aka cafke tun ranar 27 ga watan yuni,zai samu sukunin komawa gida Mombasa dake Kenya ba,bayan sauke kimanin tone 850 na shinkafa da kasashen Jamus da Japan suka bada tallafi.