1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaá tura dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD zuwa kasar Congo

April 10, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2T

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya bada sahalewa ta tura dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa su kimanin 800 daga Burundi zuwa jamhuriyar dimokradiyar Congo domin taimakawa shirin gudanar da zabe a kasar. Kwamitin tsaron mai wakilai 15 ya zartar da kudirin tura dakarun kiyaye zaman lafiyar ne na dan takaitaccen lokaci na watanni biyu. Rundunar ta kunshi zaratan sojoji 720 daga kasar Pakistan da wasu jamián sojin na majalisar dinkin duniya su 50 wadanda ke aikin sanya idanu domin tabbatar da zaman lafiya da kuma tawagar likitoci daga kasar Jordan. Zaben wanda shi ne na farko a kasar jamhuriyar dimokradiyar Congo a tsawon shekaru 40 da suka gabata, zai kawo karshen rikicin siyasa a kasar tun bayan da aka kaddamar tsare tsaren mika mulki hannu fara hula a shekara ta 2003 bayan kawo karshen yakin basasar kasar. Yan takara 32 wadanda suka hada da shugaban kasar na yanzu Joseph Kabila suka sami rajistar tsayawa takara. A ranar 19 ga wannan watan ne ake fatan tsayar da takamammen ranar da zaá gudanar da zaben.