1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

April 28, 2009

A wannan makon jaridun Jamus sun mayar da hankali ne akan zaɓen Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/Hfe1
Jacob Zuma ya ci nasarar zaɓeHoto: AP


A wannan makon dai zaɓen Afirka ta Kudu shi ne ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus dangane da nahiyarmu ta Afirka. Misali jaridar Süddeutsche Zeitung tayi amfani da wannan dama domin duba halin da mutane ke ciki a yankunan baƙar fata na ƙasar a cikin wani rahoton da ta gabatar ƙarƙashin taken: "Mazaunin 'yan rabbana ka wadata mu". Jaridar ta ce:


"Duk wanda ya kai ziyara yankimn bakar fata na Alexandra dake birnin Johannesburg ya gane dalilan da ya sanya aka gaza wajen tsamo mazauna yankin daga mawuyacin hali na rayuwa duk da nagartattun manufofi na gwamnati. Wannan yanki na daga cikin yankunan baƙar fata dake ci gaba da tunasar da gwamnatin Afirka ta Kudu da irin jan aikin dake gabanta a fafutukar yaƙi da talauci. Yankin na Alexandra na fata da ɗimbim marasa aikin yi, waɗanda dukkansu matasa ne da ka iya zama barazana ga makomar zaman lafiyar ƙasar.


Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung a cikin nata sharhin cewa tayi:


"A idanun ƙasashen Turai dai Afirka ta Kudu ƙasar ce dake da cikakken ci gaba, wadda ta ƙunshi kyawawan hanyoyi na sadarwa da bunƙasar tattalin arziki. A taƙaice Afirka ta Kudu kamar wata ƙasa ce ta Turai dake nahiyar Afirka. Gwamnatin da aka naɗa bayan kawo ƙarshen mulkin wariya tayi amfani da abubuwan da ta gada daga farar fata domin kyautata makomar ƙasar bisa saɓanin Zimbabwe. Ƙasar na samun kyakkyawan ci gaba a mulki na demoƙraɗiyya. To sai dai kuma a nan ne take ƙasa tana dabo. Domin kuwa akwai saɓani matuƙa ainun a game da sabon shugaban jam'iyyar ANC Jacob Zuma, wanda ba wanda ya san tahaƙiƙanin alƙiblar da ya fuskanta."


Al'amura sai daɗa yin tsamari suke yi a lardin Kivu na Janhuriyar Demoƙraɗiyyar Kongo inda dakarun sa kai na 'yan Hutu ke muzguna wa farar fula a cewar jaridar Die Tageszeitung. Jaridar ta ce:


"Murna ta sake komawa ciki dangane da fatan da aka yi na samun zaman lafiya a gabacin Janhuriyar demoƙraɗiyyar Kongo. Dakarun sa kai na FDLR dake da alhakin kisan kisan kiyashin ƙasar Ruwanda a shekara ta 1994 sun ƙara ƙarfafa hare-harensu a lardin arewacin Kivu a kwanakin baya-bayan nan. A ƙarshen makon da ya wuce sai da suka kai hari tare da ƙone gidaje 255 da kuma halaka mutane shida abin da ya haɗa da yara ƙanana biyar a wani ƙauye wai shi Loufu dake arewacin Kivu. Amma fa kafin hakan ya faru sai da su kansu sojojin gwamnati dake fama da yunwa suka shiga wawason ganima. A dai halin da ake ciki yanzu al'umar yankin na cikin hali na tsaka mai wuya tsakanin dakarun tawaye da sojojin gwamnati."


To ko shin ana fasa kwabrin makamai daga Libiya zuwa Darfur ta Sudan, wannan wata ayar tambaya ce da jaridar Die Tageszeitung ta gabatar dangane da shirin Libiya na sayen makamai daga Belgium. Jaridar ta ce:


"An fuskanci cece-kucen siyasa a Belgium sakamakon shirin Libiya na sayen makamai na euro miliyan 11 da dubu ɗari biyar daga ƙasar. Dalilin haka kuwa shi ne haufin da ake yi na cewar wannan wata dabara ce ta amfani da Libiya don shigar da makaman zuwa lardin Darfur na Sudan mai fama da rikici."


Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu