1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓe a Chile

December 14, 2009

Sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Chile

https://p.dw.com/p/L1rV
Sebastian PineraHoto: dpa

Bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ƙasar Chile yanzu dai ta tabbata wani attajiri mai ɗan jari hujja Sebastian Pinera ne ya samu kashi 44 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa akan abokin haimayar sa na jam'iyar dake mulki kuma tsohon shugaban ƙasa Eduardo Frei wanda ya samu ƙasa da kashi 30.

Sakamakon zaɓen na ƙasar Chile dake yankin latin Amurka ba ƙaramin gazawa bane ga jam'iyar dake mulki mai ra'ayin sauyi, ganin cewar kayin da jam'iyar dake kan karagar mulki tasha, shine irin sa na farko tun bayan da Sojoji suka miƙa ragamar shugabanci ga fararen hula a shekaru 20 da aka shafe ana mulkin demokiraɗiyya a ƙasar.

Abunda shima ɗan takarar daya samu nasara a zagayen farko na zaɓen Sebastian Pinera ya bayyana ga magoya bayan sa, Inda yake mai cewar:

" a yau al'umar chile sun bamu nasarar zaɓe. Don haka ina kira gare ku damu nuna sanin yakamata, musan cewar wannan nasara ce ga ɗokacin al'uman mu ta chile ba wai na wani ɓagare ɗaya ba.a'a nasace ta mutanen chile."

Sai dai kuma duk da wannan nasara da Pinera ya samu akan abaokan hamaiyar sa, bai samu adadain ƙuri'un da ake buƙata na fiye da kashe hamsin cikin ɗari ba, don haka dole a gudanar da zaɓe zagaye na biyu tsakanin sa da ɗan takarar jam'iyar dake mulki kuma tsohon shugaban ƙasar Eduardo Frei, wanda za'a gudanar a ranar 17 ga watan janairun baɗi.

Zaɓen da kuma babu tantama masu sharhin siyasar ƙasar ta Chile ke baiwa Pinera mai shekaru 60 a duniya kuma wanda Mujallar Forbes ta 'yan jari Hujja ta sanya sunan sa cikin jerin attajirai 700 da suka fi kowa kuɗi a duniya. Saɓanin ɗan takakar jam'iyar dake mulki ta shugabar ƙasa mace mai farin Michelete Bachalet wanda tsarin mulki ya hanata tsayawa bayan ƙare wa'adin ta. Carlos Huneeus wani mai sharhin harkokin siyasa ne a chile kuma yayi bayani kamar haka.

yace"wannan shine karon farko daga cikin ɗokacin yan takarar da suka tsaya wannan zaɓe,babu wanda ya nuna wata adawa da gwamnati maici yanzu. kuma akwai alamun dake nuna cewar kashi 60 cikin ɗari na wayanda suka zaɓi Pinera magoya bayan jam'iyar dake mulki ne"

Zaɓen ƙasar ta Chile dai ta aike da wani saƙo ga sauran ƙasashen yankin wajen samun nasarar ƙarɓe mulki daga hannun gwamnatin dake mulki, wayanda al'umar ƙasar ke ganin bata tabuƙaw ani abun azao a gani ba a shekarun da ta shafe tana mulki, duk kuwa da ɗinbin arzikin ƙarfen jan ƙarfe da Allah ya albarkaci ƙasar dashi. jam'iyar da kuma ada ta samu goyoyn bayan jam'ar ƙasar dake tausaya mata bisa yarda yayanta suka sha azaba a hannun tsohon shugaban mulki kama karya janar Augusto Pinochet.

Kamar yadda Wani Masanin harkokin Siyasa Ricardo Israel yake cewar:

yace" idan akayi la'akari da matsayin da chile ta kai, aka sarin al'amuran yau da kullum sun lalace matuƙa, abinda yasa ƙasar ke zama tamkar wata nakiya ce dake gaf da fashewa.Musanman idan akayi la'akari da ban bancin dake tsakanin masu arziki da marasa shi, yana yin ya ƙara arzuka masu kuɗi ne tare da talauta mara shi tare kuma da komabayan harkokin jin daɗin al'umma."

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou