1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓe a Mozambik

Halimatu AbbasOctober 28, 2009

A yau ne ake gudanar da zabukan shugaban ƙasa da majalisar dokoki da gudunmomi a ƙasar Mozambik

https://p.dw.com/p/KHQ0
Yaƙin neman zaɓe a MozambikHoto: AP

A yau ne ake gudanar da zaɓukan majallisar dokoki, shugaban ƙasa da gudunmomi a Mozambik . A ranar Lahadin da ta gabata ne dai aka kawo ƙarshen yaƙin neman zaɓe inda magoya bayan manyan jam'iyyun ƙasar guda uku suka ka fito ka'in da na'in. Shugaban ƙasar ta Mozambique Armando Guebuza ya kammala yaƙinsa na naneman zaɓe ne a birnin Nampula da ke arewacin ƙasar. Shi ne dai ɗan takarar jam'iyyar FRELIMO wadda a da ƙungiya ce ta fafutukar samar da 'yanci daga hannun Portugal da ta yi wa ƙasar mulkin mallaka.

Yayin bukin kawo ƙarshen yaƙin neman zaɓe na jam'iyyar FRELIMO, Shugaba Armando Emilo Guebuza ya bayyana jam'iyyarsa da cewa ita ce za ta lashe waɗanna zaɓuka:

"Tuni FRELIMO ta kama hanyar samun nasara kamar yadda ta saba yi a ƙasar Mozambik. Ko shakka babu mu zamu lashe waɗannan zaɓuka."

A haƙika dai wannan iƙirari na FRELIMO na bayyana irin halin siyasa da ke wakana a ƙasar ta Mozambique.

Mozambique dai ƙasa ce da ke rashin taƙamammiyar jam'iyyar adawa. Da yawa daga masu nazari akan al'amuran siyasa sun ce tuni aka san wanda zai yi nasara a zaɓukan na majalisar dokoki, shugaba da kuma larduna da ke gudana a yau ɗin nan.Shugaba Guebuza da jam'iyyarsa ta FRELIMO dai sun kama hanyar riƙe madafun iko ko kafin shiga takarar zaɓukan.

Mutane da dama sun ɗokanta da zaɓukan wannan shekara inda a baya ga manyan jam'iyyun adawa guda uku da suka haɗa da tsohuwar ƙungiyar 'yan tawaye ta RENAMO akwai jam'iyyar MDM wadda ake yi wa kallon hadarin kaji ganin cewa babu wata rawa ta azo a gani da za ta taka a zaɓen majalisar dokoki. Saboda cewa sakamakon kuskuren da aka samu wajen cike takardun shiga takara, a gundumomi huɗu kawai ne jam'iyyar ta MDM za ta yi takara daga cikin gudummoin ƙasar guda 13.

Kamar dai sauran takwarorinsa matasa da kuma wayyayu 'yan ƙasar ta Mozambique dai, Ärdio Evariso wanda matashi ne da ke zaman kakakin jam'iyyar MDM na mai ra'ayin cewa da wuya su samu galaba akan jam'iyyun FRELIMO da RENAMO:

"Yace dimukuraɗiyar Mozambique dai tana cikin wani hali na tsaka mai wuya, saboda cewa a ko da yaushe tsoffin jam'iyyun FRELIMO da RENAMO ne suke mata babakere. Amma kuma ba su bin tafarkin dimukuraɗiya. Sun yi biris da al'umma tare da mamaye dukkan madafun iko a faɗin ƙasar. Babu wata dimukuradiya ta haƙiƙa. Da fatar baka ne kawai suke iƙirarin kafuwar dimukuraɗiya tare da ɗaukar sauran al'umma tamkar 'yan rakiyar dimukuraɗiya."

Masu sharhi akan al'amuran siyasa na da ra'ayin cewa Mozambik dai ƙasa ce da ƙasashen wajen ke ɗauka tamkar wadda ta fi kowacce samun nasara a fannin siyasa a yankin kudancin Afirka. A ma Turai gwamnatin ƙasar ta Mozambique na shan yabo sakamakon shirinta na yaƙi da talauci. A sabo da haka ne ma aka ƙara kason da ake bai wa ƙasar daga kuɗin taimakon raya ƙasashen masu tasowa. Sai dai kuma matsalar itace yadda za a iya kau da matsalar cin hanci da rashawa da ta yi ƙasar katutu.

Pater Arlino Pinto malami ne a jami'ar Katolika da ke birnin Nampula. A nasa ra'ayin dai shugabannin siyasar ƙasar ne kaɗai ke cin moriyar manufar samar da ci gaba:

"Kashi 60 daga cikin ɗari na kasafin kuɗin gwamnatin Mozabik yana fitowa ne daga tallafin da take samu daga ƙasashen ƙetare da suka haɗa da Ƙungiyar Tarayyar Turai, Japan, Jamus, Sweden, Denmark Italiya da ragowarsu. Daga wannan kafa ne gwamnatin ke samun kuɗi ba tare da ta koma biyansu ga waɗanda suka bata ba. Inda kuwa gwamnatin na amfani da su ta taimaka wa al'umma da sun fita daga ƙangin talauci da suka tsinci kansu ciki a halin yanzu."

A ra'ayin masu sa ido akan al'amuran siyasa dai babu wata sakiya da za a samu daga zaɓukan na yau. Akasarin masu bayyana ra'ayinsu game da alamura yau da kullum sun ce babu abin da jam'iyyar FRELIMO da Shugaba Armando Emilo Guebuza ke buƙata illa sabonta halacinsu na ci gaba da riƙe ragamar shugabancin ƙasar.

Mawallafi: Cascais/Halimatu Abbas

Edita: Abdullahi Tanko Bala

Oton-Atmo