1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓe a Nigeria

April 14, 2007
https://p.dw.com/p/BuNk

Bayan taci ba ta ci ba, da a ka sha tabkawa a game da zaɓe a Taraya Nigeria, a karshe dai yau ne Al´ummomin ƙasar fiye da milion 60, da a ka yiwa rijista, za su kaɗa ƙuri´ar zaɓen gwamnoni 36, da kuma yan majalisun jihohi.

Ta la´akari da zullumi, da fargaba da al´umma ke ciki, na wanzuwar wannan zaɓe cikin lumana gwamnatinTaraya ta bayyana ɗaukar matakan tsaro ƙwaƙƙwara, ta kuma yi kira ga al´ummar kasa, ta fito ta kaɗa ƙuri´a ba tare da faɗuwar gaba ba.

Na da yan mitina ƙalilan ne za a buɗa runfunan zaɓe.

A faɗin ƙasar baki ɗaya, babu shiga babu fita, yau ta iyakokin ƙasa.

Sai ku biwo mu a cikin shirin inda za mu kawo maku bayanai, a game da zaɓen na Nigeria.