Zaɓen ƙasar Gini
June 28, 2010Talla
Masu sa ido a zaɓen ƙasar Gini da ya gudana a ranar Lahadi, sun kwatanta zaɓen na Konakry a matsayin wanda ya gudana cikin adalci. Masu sa idon daga ƙungiyar Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka haɗe da ƙungiyar haɓaka tattalin arzkin ƙasashen Afirka Ta Yamma wato ECOWAS duk sun yaba da zaɓen, wanda shi ne zaɓen shugaban ƙasar Gini na farko, da babu hannun soji tun samun 'yancin ƙasar a shekara ta 1958. An bayyana samun fitowar ɗimbin masu kaɗa ƙuri'a a ƙasar dake yammacin Afirka. Ana dai sa ran kaiwa zagaye na biyu a watan gobe, domin bisa dukkan alamu babu wanda zai samu nasara kai tsaye. Izuwa jibi ne dai ake sa ran samun sakamakon zaɓen daga hukuma.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal