1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen ƙasar Italia

April 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2B

Ƙasar Italia, ta shiga wani ƙika na siyasa, a sakamakon zaɓen yan majalisun dokoki da aka gudanar, ranekun lahadi da litinin da su ka wuce.

Sakamakon wannan zaɓe, ya ba gungun jam´iyun adawa bisa jagorancin Romano Prodi, ɗan ƙwarya ƙwaryan rijnjaye.

To saidai, shugaba mai barin gado Silvio Berlusconi, ya ƙi amicewa da wannan sakamako.

Ya kuma bukaci a sake ƙidayar kuri´u a wasu wurare.

Jiya, opishin ministan cikin gida, a hukunce, ya bayana nasara Romano Prodi, tare da samun kujeru 158, bisa jimmilar kujeru 315, da majaliasar dokokin Italia, ta ƙunsa.

Sannan, ya samu rinjaye a Majalisar dattawa, tare da kujeru 342 ,bisa jimilar kujeru 630.

Romano Prodi, tsofan shugaban hukumar zartaswa ta ƙungiyar gamayya turai, ya bayyana cewar, babu tababa shi ya lashe zaɓe.

Tunni, har ya fara samun sakwannin taya murna, daga sassa daban-daban na dunia.

A ranar yau laraba ya samu sakwanin barka da arziki, daga Praministan, Luxemburg Jean Claude Junker, da shugaban kasar France Jaques Chirac, da kuma shugaban hukumar majalisar kungiyar gamaya turai, Jose Manuel Barrosso.

A sahiyar yau ,wani komiti na mussaman ya fara sake ƙidayar kuri´un, da a ke taƙƙadama a kan su.