1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen gaba da wa´adi na ´yan majalisar dokoki a Denmark

November 13, 2007
https://p.dw.com/p/CAnF
A yau ne ake gudanar da zaben ´yan majalisar dokoki a kasar Denmark. Hakika da sai farkon shekara ta 2009 wa´adin aikin majalisar kasar da ke zaman memba a KTT ke karewa, amma FM Anders Fogh Rasmussen ya shirya zaben watanni 15 gabanin lokacin yin sa. Binciken jin ra´ayin masu kada kuri´a da aka gudanar baya bayan nan ya yi nuni da cewa jam´iyar FM Rasmussen na kan gaban ta ´yan adawa da tazarar da ba ta taka kara ta karya ba. Muhimman batun da ya fi daukar hankali a lokacin yakin neman zabe shi ne na ba tallafi ga marasa karafi, wanda ´yan adawa ke son a fadada shi, sun yi watsi da shirin gwamnati na rage haraji.