1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen gama gari a Habasha

May 29, 2010

Jaridun sun kuma taɓo mawuyacin halin da ake ciki a Afirka Ta Tsakiya

https://p.dw.com/p/Ncjj
'Yan adawa sun yi kira da a sake gudanar da sabon zaɓeHoto: DW

Daga cikin batutuwan da suka shiga kannun rahotannin jaridun Jamus dangane da nahiyar Afirka a wannan makon dai har da halin da ake ciki a game da zaɓen ƙasar Habasha. A cikin nata rahoton jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Ƙasashe da dama suka yi kakkausan suka akan zaɓen majalisar dokokin da aka gudanar a ƙasar Habasha ƙarshen makon da ya gabata, inda jam'iyyar dake mulki ta EPRDF ta samu gagarumin rinjaye. Sai dai kuma a wannan karon 'yan hamayya ba su yi kiran zanga-zanga ba, sai dai suka nema da a sake sabon zaɓe. A dai zaɓen da aka gudanar a shekara ta 2005 mutane sama da metan suka yi asarar rayukansu lokacin zanga-zangar adawa da sanarwar da jam'iyyar EPRDF ta gwamnati ta bayar na lashe zaɓen da gagarumin rinjaye."

A baya ga ƙasar Habasha jaridar ta Die Tageszeitung ta kuma leƙa janhuriyar Afirka ta Tsakiya, wadda ta ce sai ƙara shiga mawuyacin hali na ƙaƙa-nika-yi take yi sakamakon yaƙe-yaƙe na basasa da kuma dubban ɗaruruwan 'yan ƙasar dake kan hanyar gudun hijira. Jaridar ta ƙara da cewar:

Wahlen in Bangui Zentralafrikanische Republik 2005
Dogon layin masu kaɗa ƙuri'a a birnin Bangui lokacin zaɓen gama gari a Afirka Ta Tsakiya a sherarar 2005Hoto: AP

"Rikicin Janhuriyar Afirka ta Tsakiya dai wani bala'i ne dake sauka wa ƙasar sannu a hankali. A misalin shekara ɗaya da rabi da suka wuce an samu lafawar ƙura bayan da aka cimma daidaituwa tsakanin ƙungiyoyin tawaye guda biyar a ɓangare guda da gwamnatin shugaba Francois Bozize a ɗaya ɓangaren. Amma ba a daɗe ba murna ta sake komawa ciki. A sakamakon hali na ɗar-ɗar da ake ciki aka soke zaɓen ƙasar da aka shirya gudanarwa ranar sha shida ga watan nan na mayu."

Ita kuwa Nijer kamar yadda jaridar Süddeutsche Zeitung ta nunar, tana fuskantar wata barazana ta yunwa kuma a sakamakon haka ƙungiyoyin agaji ke bakin ƙoƙarinsu wajen kyautata ayyukan noma a ƙasar ta yankin Sahel. Jaridar ta ƙara da cewar:

Niger Hungerkrise
Matsalar yunwa a Janhuriyar NijerHoto: AP

"An samu hauhawar farashin kayan masarufi na yau da kullum ko da yake galibi ummal'aba'isin wannan tsadar kaya su ne 'yan baranda daga maƙobciyar ƙasa ta Nijeriya. Amma kuma a ɗaya hannun Nijer ƙasa ce da ta sha fuskantar matsaloli na yunwa, a sakamakon haka ƙungiyoyin taimako ke bakin ƙoƙarinsu wajen binciko ire-iren shuka da suka fi dacewa da yanayin ƙasar mai fama da yaɗuwar yashi. Kuma ko da yake gwamnati ta fara raba kaya abinci tsakanin jama'a, amma fa hakan ba zai wadatar ba, saboda ainihin matsalar ta ƙarancin abinci tana da nasaba ne da bunƙasar yawan jama'a na sama da kashi uku cikin ɗari da Nijer ke samu a kowace shekara."

Wani kamfani na sojan haya mai zaman kansa na shirin tura tsaffin sojoji da 'yan sandan Jamus zuwa Somaliya mai fama da yaƙin basasa. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Der Tagesspiegel cewa tayi:

"Ƙwararrun masana al'amuran tsaro sun yi nuni da cewar ba za a iya hana tsaffin sojoji da 'yan sandan ba da kansu haya ba. Akwai ma bayanai dake nuna cewar akwai tsaffin dakarun kwantar da tarzoma na sojan Jamus na wa kamfanin sojan haya na Amirka Blackwater aiki. Akwai dai masu fargabar cewa za a riƙa neman yin garkuwa da Jamusawan don neman yi wa gwamnatin ƙasar ci da ceto ko kuma dakarun al-Ƙa'ida su yi amfani da su a ƙoƙarin tilasta wa Jamus ta janye sojojinta daga Afghanistan."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal