1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

150108 Superwahljahr

Mohammad AwalJanuary 18, 2009

A yau Lahadi ake gudanar da zaɓen ´yan majalsiar dokokin jihar Hesse matakin farko a jerin zaɓuɓɓukan da za a gudanar a tarayyar Jamus a wannan shekara.

https://p.dw.com/p/GagA
Roland Koch, Firimiyan jihar HesseHoto: AP

Wannan zaɓen ya zo ne ƙasa da shekara guda bayan zaɓen ´yan majalisar dokokin jihar ta Hesse da aka gudanar a ranar 27 ga watan Janerun shekara ta 2008, inda ba bu wata jam´iya da ta samu rinjaye balantana ta kafa gwamnati. Wannan halin da ake ciki a majalisar dokokin jihar shi ne irinsa na farko a Jamus.

A halin da ake ciki Jamusawa na kwatanta halin siyasar da ake ciki a jihar ta Hesse da gazawar ´yan siyasa wajen kafa gwamnati bayan zaɓe. Da wahala wajen kafa gwamnati a wata majalisa mai wakilcin jam´iyu guda biyar ba kamar a da ba inda ake da wakilcin jam´iyu huɗu ko uku. A zaɓen ´yan majalisar dokokin jihar ta Hesse a bara babu ɗaya daga cikin manyan jam´iyu da ta samu rinjaye da zata kafa gwamnati ita kaɗai, ko ƙulla ƙawance da wata ƙaramar jam´iya. da zai yiwu a ƙawance tsakanin CDU da SPD kamar yadda yake a wasu jihohin musammman ma a gwamnatin tarayyar ƙarƙashin jagoran Angela Merkel to amma an hana yin haka a jihar ta Hesse. A majalisar dokoki ta tarayya ma yanzu ba ɗaya daga cikin manyan jam´iyun da take da rinjaye. Wato kenan babban ƙawance za ta zama zakaran gwajin dafi a zaɓen ´yan majalisar dokokin tarayya da zai gudana a ranar 27 ga watan Satumba na wannan shekara. Sakamakon taƙadamar da ake yi na gano mafita daga matsaloli tattalin arziki, tuni dai aka fara yaƙin neman zaɓe.

"Dukkan mu mun san wannan shekarar tana tattare da manyan ƙalubaloli"

kalaman shugabar gwamnatin Jamus kenan Angel Merkel lokacin da take ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe. Ɗan takarar neman shugaban gwamnatin Jamus ƙarƙashin jam´iyar SPD Frank-Walter Steinmeier wanda har wa yau shi ne ministan harkokin waje a cikin gwamnatin Merkel ya gabatar da kansa a matsayin wanda zai daidaita al´amura yana mai cewa.

"Bai kamata shekara ta 2009 ta zama shekara ta korar ma´aikata ba."

Duk da yaƙin neman zaɓe na tarayya jam´iyun CSU da CDU da kuma SPD na haɗa kai don magance matsalolin da ake fuskanta saɓanin a jihar Hesse inda ake ƙara samun ɓaraka tsakanin jam´iyar CDU ´yar ra´ayin mazan jiya ƙarƙashin Firimiya Roland Koch da masu neman canji na jam´iyar SPD a Hesse. Sau biyu shugabar su Andrea Ypsilanti ta kasa cimma burinta na kifar da gwamnatin Firimiya Koch ta hanyar ƙulla ƙawance da juriya da masu ra´ayin canji. Ana ɗaukar wannan matakin da rashin cika alƙawari a ɓangaren SPD. Sabon ɗan takarar SPD a zaɓen na Hesse Thorsten Schäfer-Gümbel ya daɗe yana nesanta kanshi daga wannan mataki.

Ya ce. "Mun koyi darasi daga waɗannan kurakurai. Saboda haka aka tsayar da sabbin ´yan takara a zaɓen majalisar dokokin Hesse. Kuma Andrea Ypsilanti ta ɗauki alhakin abin da yaru kuma ta ce ba ta son mu taɓo wata magana dangane da rashin cika alkawari a yaƙin neman zaɓe."

Schäfer-Gumbel dai na kaucewa yin magana game da ƙulla ƙawance wato kenan ba ya son a zarge shi da rashin cika alƙawari. Amma ga Roland Koch wannan wata dabara ce ta siyasa. Ƙuri´ar jin ra´ayin jama´a da aka yi ta nuna cewa Koch ka iya ƙulla ƙawance da FDP domin ya samu rinjayen ci gaba da ɗarewa kan mulki.