1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen kansiloli a Burkina Faso

April 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0r

Bayan watani 6 da zaɓen shugaban ƙasa, yau ne a Burkina Faso al´umma ta gudanar da zaɓen kansiloli .

Kimanin mutane kussan milion 4 ne, ya cencenta su kaɗa kuri´u, domin zaɓen wakilai kussan dubu 18,a majalisun jihohi da na ƙananan hukumomi, da yawan su ya tashi 351.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta, ta buɗa runfunoni kussan dubu 13, a faɗin ƙasa baki ɗaya, domin gudanar da wannan zaɓe.

Sannan jam´iyun siyasa 73 su ka fafatawa a zaɓen.

Rahotani daga Wagadugu baban birnin ƙasar, sun nunar da cewa, an gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin kwanciyar hankali, sannan, zaɓen na yau, ya wakana salin alin.

Mutane sun fito da dama, domin kaɗa ƙuri´a.

Wannan zaɓe na matsayin matakin ƙarshe, na shinfiɗa mulkin demokradiya a ƙasar Burkina Faso.