1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen kundin tsarin mulki a Mauritania

Yahouza Sadissou MadobiJune 23, 2006

Ranar lahadi al´ummar ƙasar Mauritania ke zaɓe a game da saban kundin tsarin mulki

https://p.dw.com/p/Btze

Ranar lahadi ne idan Allah ya kai mu, a ake kaɗa ƙuri´ ar jin ra´ayin jama´a a ƙasar Mauritania, a gema da saban kundin tsarin mulki, da gwamnatin riƙon ƙwarya ya tsara.

Da farko dai,Jamhuriya musulunci ta Mauritania, na da yawan al´umma milion 3, kuma ƙasar ta samu yancin kai tun shekara ta 1960 daga turawan mulkin mallakar ƙasar Fransa, bisa jagorancin Mokhtar Uld Daddah.

Rigingimmun ƙabilanci da na siyasa, sun hadasa yawan juyin mulki, da kuma tashe tashen hankula,masu nasaba da ƙabilaci.

Na baya bayan nan, shine wanda shugaban mai ci yanzu Ely Uld Mohamed Vall, ya kitsawa shugaba Mu´awiya Uld Taya, ranar 3 ga watan oktober na shekara ta 2005.

Sojojin da su ka jagorancin wannan juyin mulki ,sun bayana aikata hakan, domin taka birki ga mulkin danniya, da kama karya, da shugaba Uld Taya ya shinfiɗa fiye da shekaru 20.

Kazalika, sun alƙawarta shinfiɗa demokradiya ingantata a wannan ƙasa.

Don cimma wannan alkawari, sojojin su ka girka hukumar adalci da demokradiya, da su ka radawa suna CMJD.

Hukumar, ta shirya tarruruka da ɓangarori daban-daban na ƙasar, da su ka haɗa da jam´iyun siyasa da ƙungiyoyin fara hulla, domin cimma matsaya ɗaya, a game da sabon daftarin mulki, da jibi inda Allah ya kai, mu jama´a, zata kaɗa ƙuri´ar amincewa kokuma watsi da shi.

Wannan saban kudi, ya kawo cenje cenje da dama, ga tsofan wanda a ke aiki da shi tun shekarta ta 1991.

A dangane da addadin zama kan karagar shugabacin kasa, kundin ya tanadi shekaru 5, sannan shugaban da aka zaɓa,ɓa shi da izinin ajje takara fiye da sau 2,wato ba za shi wuce shekaru 10 ba,bisa kujera mulki, ayainda wacen kudin ya ba shugaban damar zama bisa har inda mai ya ƙare.

Sannan shekarun shugaban ƙasar za su kasance tsakanin 40 zuwa 75.

Ta la´akari da cewa, dama daga shugabanin Afrika na gudanar da kwaskwarima ga kundin tsarin mulki domin yin tazarce, Mauritania ta ɗauki mattakai, inda sai shugaban kasa yayi rantsuwa da Al´ƙur´ani mai girma ,a kann cewar ba zai taɓa komai ba, daga cikin kundin a zahiri ko a baɗini,da nufin yin tazarce.

Saban kundin tsarin mulkin, ya ƙunshi yanayin mulkin mai ruya ɗaya, inda shugaban ƙasa ke da cikkaken mulki cikin hannun sa, tare da naɗa Praminista, to saida Majalisar Dokoki na da yancin kaɗa kuri´ar sabke praminstan muddun buƙatar hakan ta taso.

Sannan saban kundin tsarin mulkin ya haramtawa shugaban ƙasa gudanar da harakokin siyasa, saɓanin wanda ya gabata, inda shugaban Uld Taya ke riƙe da shugabancin jam´iyar sa.

An dangane da karbuwar kundin ga wakilan jama´ar ƙasa shugaban jam´iyar gurguzu mai adawa Messaud Ould Bouhkeir yayi bayani kamar haka:

Kussan ɓangarori baki ɗaya sun yi na´am da saban kundin, wanda a cikin sa, a ka rage wa´adin zama kan karagar shugabancin ƙasa, sannan a ka yi tanade tanade da dama, na ƙarffafa demokradiya.

To saidai akwai wasu ƙananan jam´iyu guda 2, da su kayi kira ga magoya bayan su , da su kaɗa kuri´ar ƙin amincewa da kundin, shugaban ɗaya daga wannan jam´iyu Mamadou Alassane, ya bayyana dalilan da su ka sa ɗaukar wannan mataki:

Ba mu gamsu ba, da kundin tsarin mulkin , sabo da dokokin da ya ƙunsa , basu dace ba ,da matsalolin Mauritania.

Mun buƙaci a rubuta ɓallo –ɓallo cewar,, Mauritania ƙasa ce da ta ƙunshi ƙabilun larabawa, hillani, Soninke da Wollof, sannan harsunnan ƙasar an mayar da su, ba bakin komai ba a cikin kudin.