1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

040908 Angola Parlamentswahl

Cascais, Antonio Luanda DW Portugiesisch September 5, 2008

Wannan zaɓen shi ne karon farko a Angola tun kimanin shekaru 16 da suka wuce

https://p.dw.com/p/FBqx
Magoya bayan UNITA babbar jam´iyar adawa a AngolaHoto: picture-alliance/ dpa

A yau ne masu kaɗa ƙuri´a a Angola su kimanin miliyan 8.5 ke zaɓen ´yan majalisar dokoki karo na biyu tun bayan shekarar 1992. Ko da yake hukumar zaɓe ta ba da tabbacin cewa za a yi zaɓen gaskiya da adalci wato saɓanin yadda ya kasance a ƙasashen Kenya da Zimbabwe ba, to amma masu sa ido a zaɓe sun nuna shakku ga wannan iƙirarin.


Yayin da jam´iyar MPLA mai jan ragamar mulkin ƙasar ta Angola tun bayan samun ´yancinta daga ƙasar Portugal shekaru 33 da suka wuce ta ƙara ƙarfi a lokaci guda kuma jam´iyar ta shugaban ƙasa mai cikakken iko Jose Eduardo dos Santos ba ta shirin raba iko da ´yan adawa da sauran ƙungiyoyin jama´a. Saboda haka ba abin mamaki ba ne da aka yi amfani da wasu hanyoyi da ba su dace ba wurin yaƙin neman zaɓe.


Shugaba Jose Eduardo dos Santos a wani gangamin zaɓe a birnin Luanda inda ya ke cewa: "Abu ɗaya muke so wato ƙuri´ar ´yan Agola ga jam´yiar MPLA. Allah Ya ja zamin MPLA. Ana ci-gaba da gwargwarmaya kuma nasara ta na gare mu."

Ɗaiɗaikun jam´iyu 10 da kuma na kawance guda huɗu ke takarar zaɓen na shiga majalisar dokokin ƙasar ta Angola mai kujeru 320. Sannan a baɗi idan Allah Ya kaimu za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasar. Bisa abubuwan da suka wakana a lokacin yaƙin neman zaɓen na ´yan majalisa ana iya hasashen yadda zaɓen shugaban ƙasar zai kasance a baɗi wato inda shugaba Dos Santos zai zama tamkar shi ne wuƙa shi ne nama. A halin da ake ciki shi ke iko da fagen siyasar ƙasar da kafofin yaɗa labaru, tattalin arziki da kuma batulmalin gwamnati. An kashewa jam´iyar maƙudan kuɗaɗe yayin da ´yan adawa suka tashi a tutar babu. Saboda haka magoya bayanta suka yi imanin lashe zaɓen na yau da gagarumin rinjaye, kamar yadda wani ɗan gani kashenin jam´iyar MPLA ya nunar.

Ya ce: "Yau rana ce mai muhimmanci a garemu. Muna jinjinawa shugaban MPLA. Tun yanzu mun sa cewa jam´iyar ta riga ta yi nasara. Jira muke yi kawai a kammala kaɗa ƙuri´a."

Babbar jam´iyar adawa ita ce tsohuwar ƙungiyar ´yan tawaye ta UNITA wadda tun a 1992 ta ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnati, to ama bayan zaɓe na wancan lokaci wani sabon yaƙin basasa ya sake ɓarkewa, sai bayan mutuwar shugabanta Jonas Savimbi a shekara ta 2002 zaman lafiya ya wanzu a Angola.


A lokacin yaƙin neman zaɓe magoya bayan shugaban kasa sun ta tursasawa ´yan adawa sannan an hana su damar yin kamfen ta kafofin yaɗa labarun hukuma. Saboda haka ne ma ´yan adawan da jami´an sa ido a zaɓe ke da ra´ayin cewa a cikin irin wannan yanayi ba za a yi adalci a zaɓen ba.


A halin da ake ciki cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a ƙasar yayin da giɓi tsakanin matalauta da masu arziki ke ƙaruwa. Hakan kuwa na faruwa duk da ɗinbim arzikin man fetir da kasar ke da shi.