1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen Majalisar Turai

June 8, 2009

Waiwaye adon tafiya dangane da zaɓen Majalisar Turai

https://p.dw.com/p/I5U2
ZaɓeHoto: AP

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta zaɓi sabbin wakilan majalisarta. Bisa ga sakamakon zaɓuɓɓukan dai Masu tsattsauran ra'ayi na nahiyar su ne suka samu rinjaye. Ayayinda masu sassaucin ra'ayin kishin ƙasa suka samu matsayi na biyu, sai masu matsakaicin ra'ayin sassauci, kana masu fafutukar kare muhalli.

Za a iya bayyana zaɓen Majalisar Turai da aka kammala da kasancewa koma baya a ɓangaren jami'iyyun da suke mulki musamman dangane da farfaɗowan wasu jam'iyyu a nahiyar, da rashin fitowar jama'a wajen kaɗa kuri'u. Kashi 43 daga cikin 100 na waɗanda ya cancanci su kaɗa kuri'unsu ne kaɗai suka fito. Abunda kuma ke iya zama mummnan sakamako a tarihin zaɓe, da kuma abinda zai iya haifarwa a cewar mai Ɗan kallo daga nahiyar Afrika Marwick Kumalo....

" Mun fahinci cewar an tsara zaɓen sosai da yadda zai gudana, sai inda gizo ke saka shine yadda mutane basu nuna sha'awarsu wajen fitowa domin kaɗa kuri'unsu ba"

Ko dai gwamnati mai tsattsauran ra'ayi a Austria ko kuma mai sassaucin ra'ayi kamar yadda yake a ƙasar Netherland, ana iya cewar waɗannan ƙasashen biyu sun kasance abun kwatance ana nuna halayya guda. Ana iya cewar tamkar mafi yawa daga cikin masu kaɗa ku'riun sun ɗauki matakan hukunta gwamnatocinsu ne.

EU Wahlen zu EU Parlament in Brüssel Deutschland Angela Merkel und Hans-Gert Pöttering
Angela Merkel da Hans-Gert Poettering.Hoto: AP

Ƙasar Britania ta zame wani batu ne na musamman a zaben majalisar Turan, in bayan yamutsi da rigingimu a gwamnati, jami'iyyar labour ta sha kaye.

Kamar dai yadda yake a ƙasashe da dama na nahiyar, sakamakon zaɓen a Britania nada alaka ne kalilan da siyasar nahiyar Turai, wanda kuma baki daya ke ta'allaka da batutuwa da suka shafi ƙasa.

To sai dai bayan wannan zaɓen dai masu nazarin lamuran siyasa na ganin cewar, da wannan sakamakon kusan abu kalilan ne watakila zai iya sauyawa a majalisar turan.

Kuma ana iya cewa masu tsattauran ra'ayi na turan sun sake tabbatar da matsayinsu, na jammi'iyyu da suka fi karfi a nahiyar turai, fiye da masu sassaucin ra'ayi waɗanda suka sha kaye a zaɓen majalisar turan.

Sai dai kuma bayan sakamakon zaɓen,har yanzu kananan jami'iyyu sun da muhimmiyar rawa da zasu taka. Shugaban majalisar Hans-Gert Pöttering, ya bayyana tsoronsa dangane da yanayi mawuyaci da zasuyi aiki tare...

Europawahl: Hans-Gert Pöttering, CDU
Hans-Gert PoetteringHoto: picture-alliance / dpa

"Ina matukar farin ciki ganin cewar jami'iyyun dake goyon haɗin kan turai sun samu rinjaye a wannan zaɓen. Kuma ina fatan zamu yi aiki tare a wannan majalisa da sauran wakilan jami'iyyu da basu da wannan akidar, bisa ga kyakkyawan manufa. Ina taya dukkan wakilai murna "

Rashin fitowan jama'a domin zaɓe da tasowan jami'iyyun dake adawa da akidojin turai dai, batutuwa guda biyu ne da da suka razanar da wannan majalisar. Kuma a 'yan kwanaki masu gabatowa za su yi nazarin dalilin da suka jagoranci hakan.

Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Hauwa Abubakar Ajeje