1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen majalisun dokoki a ƙasar Algeria

May 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuLS

A yau yan ƙasar Algeria ke fita kaɗa ƙuriá domin zaɓar sabbin yan majalisun dokoki. Wannan shi ne zaɓen yan majalisun dokoki karo na uku tun bayan da aka soke babban zaben ƙasar a shekarar 1992. An tsaurara matakan tsaro a cibiyoyin zaben bayan wani hari bom da ya auku a jiya a birnin Constatine wanda ya hallaka ɗan sanda ɗaya ya kuma jikata wasu fararen hula biyar. Wannan shine hari mafi muni tun bayan fashewar wasu jerin bama bamai uku a Algiers babban birnin ƙasar wanda ya kashe mutane 30 da raunata wasu mutanen fiye da 200 makwanni biyar da suka wuce. Yan ƙungiyar al-Qaída sun baiyana alhakin kai wannan hari.