1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen Nijar da ke tafe na ɗaukar hankali jama'a

Salissou Boukari/AHFebruary 5, 2016

Yayin da ake ƙoƙarin cika mako ɗaya da soma yakin neman zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokoki akwai fargaba dangane da makomar zaɓen.

https://p.dw.com/p/1HqbA
Niger Wahlen Politik Stimmen Auszählung
Hoto: DW/M. Kanta

Ruɗani dai a fagen siyasar Nijarya ɗauko tushe ne tun daga yunƙurin kafa gwamnatin haɗin kan 'yan ƙasa da shugaban ƙasar mai ci Issoufou Mahamadou ya ƙudiri aniyar yi wanda bayan gaza samun jittuwa tsakanin ɓangarorin, 'yan adawar ƙasar ta Nijar a ƙarƙashin inuwar ARN suka fitar da sanarwar yin watsi da duk wani tsari na kafa gwamnatin haɗin kan 'yan ƙasa batun da dama a lokacin wasu ke yi masa kallon maƙarƙashiya ta 'yan siyasa.

Rashin fahimta tsakanin'yan siyasar na Nijar tun da ga batun kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa

Duk kuwa da cewar ba a samu fahimta ba tsakanin ɓangaran 'yan adawar da na masu mulki, amma kuma shugaban ƙasar ya yi nasarar janyo wasu daga cikin shika-shikan membobin jam'iyyun na adawa abun da ya sanya zaman doya da man ja a tsakaninsu. A jajibirin soma yaƙin zaɓen ƙasar ta Nijar, Ƙungiyar NDI ta ƙasar Amirka mai fafutukar kare demokaraɗiyya a cikin ƙasashe, ta nemi da 'yan siyasar ta Nijar su saka hannu a wani littafi da ya ƙumshi tsarin tafiyar demokaraɗiyya domin ganin an yi zaɓe lafiya kuma bayan an gama kowa ya aminta da sakamakon da za'a fitar.Sai dai kuma 'yan adawa ba su saka hannu kan wannan kundi ba bisa dalillan ci gaba da tsare abokansu a gidajan kurkuku bisa dalillai na siyasa.

Niger Mahamadou Issoufou Präsidentschaftswahlen
Mahamadou Issoufou shugaba ƙasar NijarHoto: picture alliance/Photoshot

To ko mi wakilin kungiyar ta NDI a Nijar zai ce kan wannan yanayi na zafi da ake kallon fagen siyasar ta nijar na dauka? ga dai Yanik Van Ovirbek da na shi tsokaci:

" To a gaskiya ba abin mamaki ba ne na ganin irin wannan hayaniya tsakanin 'yan adawar da masu mulki a lokacin zaɓe domin kusan a dukkan ƙasashe haka abin yake. Sai dai kuma mun yi tsamani 'yan adawar na Nijar za su saka hannu kan wannan kundi na kyaukyawar tafiya, kuma hakan ya ƙara tabbatar cewar akwai matsaloli tsakanin ɓangarorin don haka ma na ke ganin ya kyautu a ƙara sa ido dan ganin kowa ya yi biyayya ga wannan kundi."

Martanin jagoran 'yan adawar Seini Oumarou a game da halin da ake ciki a ƙasar

A cewar ɗan takarar jam'iyyar MNDS Nasara madugun 'yan adawar kasar ta Nijar yanayin ne na wannan karo ya banbanta da wanda aka saba gani:

Seini Oumarou Kandidat Wahlen im Niger
Seini Oumarou jagoran 'yan adawa kana shugaban jam'iyyar MNSD NasaraHoto: AP

" Kasar Nijar ta shirya zaɓuka da dama, kuma wani lokacin ma cikin yanayi mai wahalar gaske domin mun shirya aƙalla zaɓuka uku da suka biyu bayan mulkin riƙon ƙwarya na soja amma kuma tun da ake a ƙasar ta Nijar, ba'a taɓa ganin lokacin zaɓe mai zafi irin haka ba. Idan aka duba za a ga duk da cewar akwai wannan hukuma ta CNDP inda a nan ne muke walwale duk wasu matsaloli na fuskan siyasa, amma wannan hukuma tana nan sai dai cikin waɗannan shekaru ba ta yi aiki kamar yadda ta yi a baya ba."

Wasu dai na ganin cewar tsare shugaban jam'iyyar Lumana kuma tsofon kakakin majalisar dokokin Nijar Hama Amadou, da kuma kame wasu muƙarrabansa na daga cikin abin da ke tayar da hankula, inda wasu ke cewar ba komai ba ne illa kawai bita da kulli.