1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen shugaban ƙasa a France.

May 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuM2

Yau ne al´ummar kasar France kimanin milion 44 da rabi, ke gudanar da zaɓen shugaban ƙasa zagaye na farko.

Yan takarta 2, su ka shiga wannan zaɓe, wato Nikolas Sarkozy, na jama´iyar UMP mai riƙe da ragamar mulki, da kuma Segolene Royale ,ta jama´iyar PS mai adawa.

A dalili da tazara lokaci, tun jiya fransawa da ke wasu ƙasashen yankin Amurika, su ka gudanar da zaɓen , rahotani sun kuma nunar da cewa, sun hitto da himma.

Har lokaci kamalla yaƙin neman zaɓe ranar juma´a da ta wuce,ƙiddidigar jin ra´ayin jama´a, na bayyana Sarkozy a matsayin wanda zai gaji shugaba Jacques Chirac.

Saidai saɓanin yadda a ka zata da farko, a wannan karo ma jama´a ta hitto da himma domin kaɗa kuri´a, kamar yadda shugaban wata runfunar zaɓe ya bayyana:

„Na yi mamaki yadda mutane a wannan karo ma su ka yi tururuwa, zuwa rufunan zaɓe, duk kuwa da umurnin da wasu jam´iyu su ka bada na ƙauracewa zaɓen.

To amma duk da haka, ya na wuya yawan ƙuri´un zagaye na 2, su zarta na zagayen farko“.

A na sa ran samun sakamakon zaɓen a daidai ƙarfe 8, na daren yau, agogon France, wato ƙarfe 6 agogon GMT.