1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen shugaban ƙasa a Nigeria ya wakana cikin hargisti

April 22, 2007
https://p.dw.com/p/BuN6

Jami´an da su ka sa ido, a zaɓen shugaban ƙasa da na yan majalisun taraya, da ya wakana jiya, a Nigeria, sun buƙaci hukumar zaɓe mai zaman kanta,wato INEC, ta rusa zaben, ta kuma sake wani sabo, ta la´akari da ɗimbin kura-kuran da su ka wakana a zaɓen na jiya.

Shugaban hukumar sa ido ce, ta „Transition Monitoring Group“, Innocent Chukwuma, ya bayyana hakan, a wata hira, da kampanin dullacin labarun na Reuters.

Ita ma jami´yar AC, ta ɗan takara EL Haji Attiku Abubakar ta bayyana sanarwa, inda ta zargi INEC ta kitsa wannan kura-kurai dagangan da nufin yin murɗiya da aringizon ƙuri´u, ga ɗan takara PDP.

A yau ma, ana ci gaba da kaɗa kuri´u, a wasu ƙananan hukumomi, a yayin da kuma hukumar INEC, ta bayyana rusa zaɓen wasu yankunan.

Sai ku kasance tare da mu, nan da ɗan lokaci ƙalilan, inda za ku saurari rahottanni, daga wakilan mu a yankuna daban-daban, a game da halin da ake ciki a Nigeria.