1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen Shugaban ƙasa a Serbia

Tanko Bala, AbdullahiJanuary 21, 2008

Ɗan takarar jamíyar adawa Tomislav Nikolic ya lashe zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa a Serbia.

https://p.dw.com/p/CvYH
Tomislav Nikolic da Boris Tadic manyan yan takara biyu dake fafatawa a zaɓen SerbiaHoto: picture-alliance/ dpa


► ƙwarya-ƙwaryar sakamakon zaɓen da ya fara baiyana a yau ɗin nan ya nuna Tomislav Nikolic mai raáyin riƙau ya lashe zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ƙasar Serbia, sai dai har yanzu da sauran rina a kaba inda zai fafata da shugaba mai ci kuma mai raáyin sauyin Boris Tadic a zaɓe na gaba da zaá gudanar a ranar 3 ga watan Fabrairu.◄


A watan gobe ne dai Idan Allah ya kaimu alúmar ƙasar Serbian za su yi zube ban ƙwaryata, inda za su zaɓi tsakanin ɗan kishin ƙasa kuma ɗan mazan jiya wanda ya karkata ga Rasha da kuma ɗan takara mai sassaucin raáyin dake muradin ganin ƙasar ta juya akala ga tsarin tafarki irin na yammacin turai.


Dukkanin `yan takarar biyu dai na adawa da baiwa lardin Kosovo yancin cin gashin kai, matsayin da ake dakon bada sanarwa akai da tallafin tarayyar turai da zarar an kammala zaɓen. ´Yan takara tara ne dai suka fafata a zagayen farko na zaɓen wanda aka gudanar a jiya. Sakamakon ya nuna ɗan Mazan Jiya Tomislav Nikolic na da kashi 39.6 cikin ɗari na adadin ƙuriun da aka kaɗa yayin da abokin takarar sa Boris Tadic yake da kashi 35.5 cikin ɗari.


Gwarazan biyu za su sake fafatawa ne a ranar 3 ga watan Fabrairu, manazarta dai na ganin cewa mai yiwa tarihi ya sake maimaita kan sa, kamar yadda ya gudana a zaɓen shekara ta 2004 inda Tadic ya yi galaba da kashi 53.2 cikin ɗari na ƙuriún.


Irin yadda mutane suka yi fitowar ɗango wanda ake gani shine mafi girma a ƙasar Serbia tun bayan da aka kawar da gwamnatin Slobodan Milisevic a shekara ta 2000 ya nuna cewa mutanen ƙasar sun ɗauki wannan zaɓe da matuƙar muhimmancin gaske, kuma akwai alamun cewa jamaá za su fito sosai a zaɓe mai zuwa na ranar 3 ga watan Fabrairu. Kowanne dai daga cikin yan takarar na buƙatar yin gangamin jamaá domin su fito su kaɗa musu ƙuriá.

ga dai irin bayanin da Boris Tadic yayi ga jamaár ƙasar.


"yace wajibi ne alúmar Serbia su fito domin kaɗa ƙuriár su a ranar 3 ga watan gobe Idan Allah ya kai mu, domin nuna cewa Serbia ba zata yi watsi da manufar da ta sanyawa ɗanba a shekarar ta 2000 ba, na shiga tarayyar turai. Yana mai kashedi da a yi hattara kada a maida ƙasar baya idan suka sake Nikolic ya ci zaɓe".


A nasa ɓangaren Nikolic ya musanta zargin cewa zai maida ƙasar saniyar ware. "Yace na yi Imanin Serbia zata kasance tsakatsaki tare da yin hulɗa da ɗaukacin ƙasashe 27 na tarayyar turai da kuma Rasha wadda ita ce kaɗai ke marawa Serbia baya wajen daƙile yancin cin gashin kai ga ƙabilun Albaniyawa masu rinjaye na yankin Kosovo".


A waje guda dai ƙungiyar tarayyar turai ta jaddada matsayin ta na yin ƙawance da ƙasar Serbia. A ta bakin babban jamiín harkokin waje na ƙungiyar tarayyar turai Javier Solana, yace suna da amannar cewa zaá sami cigaba mai maána a dangantakar dake tsakanin tarayyar Turai da Serbia.


Ita ma ƙasar Jamus a ta bakin wani mai magana da yawun maáikatar harkokin wajen ƙasar Martin Jaeger yace makomar Serbia ya dogara ne ga ƙungiyar tarayyar turai kuma zaɓi ya rage ga yan ƙasar.