1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen shugaban ƙasa a Togo

March 4, 2010

Ba a fuskanci tashin hankali a zaɓen shugaban ƙasar Togo ba

https://p.dw.com/p/MJtn
Sojojin Togo na kaɗa ƙuri´a kwanaki uku gabanin zaɓeHoto: AP

Rahotanni daga kafofin yaɗa labarun ƙasar da kuma ƙungiyoyinsa ido a zaɓe na ƙasa da ƙasa sun yi nuni da cewa zaɓen ya gudana cikin yanayi na kwanciyar hankali da lumana saɓanin yadda ya kasance a zaɓukan shekara ta 2005 inda aka samu tashe tashen hankula da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Wannan zaɓe dake zaman zakaran gwajin dafi na jaririyar demukuraɗiyya wannan ƙaramar ƙasa dake yankin na yammacin Afirka kuma na biyu tun bayan mutuwar ɗan mulkin kama karyar ƙasar Gnassingbe Eyadema, ´yan takara shida ne suke fafatawa da shugaban ƙasa mai ci Faure Gnassingbe mai shekaru 43, wanda aka yi hasashen shi ne zai lashe zaɓen. Shi dai shugaba Gnassingbe wanda ke neman a sake zaɓensa karo na biyu don yin sabon wa´adin mulki shi ne ɗan tsohon shugaban ƙasar wato marigayi Gnassingbe Eyadema wanda ya mulki ƙasar tsawon shekaru 38.

Tuni dai jagoran ´yan adawa Jean-Pierre Fabre na jam´iyar UFC mai ra´ayin canji ya yi garagɗin cewa mutane ba za su amince da sakamakon wani zaɓe na maguɗi ba. Ɗan adawan ya nuna shakku ga sake samun nasarar shugaba Faure Gnassingbe. Ya ce yayi imani a wannan karon ma za a fuskanci abubuwan da suka biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar shekaru biyar da suka wuce. Ya saka ayar tambaya ga sahihancin hukumar zaɓen ƙasar. 

Menschen demonstrieren in Togo
Masu zanga-zanga a LomeHoto: AP

Tony Colgue wani ɗan jaridar ne a ƙasar ta Togo, yayi rangadi a wasu yankunan ƙasar, ya bayyana irin fatan da al´umar ƙasar ke nunawa dangane da wannan zaɓe.

"Fatan su shi ne a yi adalci a zaɓe kuma sakamakonsa ya kasance abin da mutane suka zaɓa. Yau dai kimanin shekaru 40 kenan wannan gwamnati na jan ragamar mulki kuma ko da yake Faure ya yi ƙoƙarin nunawa duniya cewa shi fa ba kamar mahaifinsa ba ne to sai dai har yanzu ba ta canza zane ba. Al´uma sun ƙosa da wannan gwamnati suna neman canji. Wato abin nufi idan abinci ya gundureka ba ka jin daɗinsa kuma."

Yaƙin neman zaɓen na wannan shekara dai ya tafi cikin kwanciyar hankali da lumana kuma masu sa ido a zaɓe daga ƙungiyar tarayyar Afirka da Tarayyar Turai da kuma ƙungiyar haɓaka tattalin arzikin ƙasashen Afirka Ta Yamma suna ƙasar inda suka shaida yadda shirye shiryen zaɓen suka gudana.

Shirya zaɓe na gaskiya da adalci cikin zaman lafiya na da muhimmanci a wannan yanki wanda ya ga juyin mulkin soji kwanan bayan nan a Janhuriyar Nijer da rigingimu a ƙasar Ivory Coast sakamakon jinkirta zaɓen shugaban ƙasar. Hinrich Küssner na ƙungiyar haɗin kai tsakanin Jamus da Afirka dake birnin Hamburg masani kan harkokin yau da kullum a nahiyar ta Afirka, ya ce duk da cewa yaƙin neman zaɓe ya fi salin alim to amma kasancewar jam´iyar gwamnati ce ta fi samun damar shiga kafofin yaɗa labaru don yin kamfen to ko shakka babu da ayar tambaya ga sahihancin wannan zaɓe.

A ziyarar da na kai Togo baya-bayan nan na ga yadda ake bawa matan karkara rance ana yi musu alƙawari cewa ba dole ne su biya bashin ba idan shugaba Faure yayi nasara. Mun samu rahotanni masu yawa game da shirin yin aringizon ƙuri´u a sassa daban daban na ƙasar."

Fischfang in Togo
Masunya a TogoHoto: picture-alliance/dpa

Togo da taɓa kasancewa ƙarƙashin mulkin mallakar Jamus tana ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya. Tana da albarkatun ƙasa da suka haɗa da sinadrin phosphate, koko, gahawa da auduga. Kusan kashi 60 cikin 100 na al´umarta da yawansu ya kai miliyan 6.6 ƙananan manoma ne da albashinsu bai fi euro ɗaya a rana ba.