1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

200809 Afghanistan Wahlen Auftakt

August 20, 2009

Ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro ne ake gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Afghanistan, 'yan sanda da sauran jami'an tsaro ɗauke da bindigogi su kusan 300,000 aka tura runfunan zaɓe a ko'ina cikin faɗin ƙasar.

https://p.dw.com/p/JF61
Jama´a a layi suna jiran su kaɗa ƙuri´aHoto: DW

Cikin ƙuri'ar jin ra'ayi da aka gudanar, shugaba Hamid Karzai shine ke gaba koda yake farin jininsa ya ragu a bayansa kuma tsohon ministan harkokin waje, Abdullah Abdullah. A wannan zaɓe dai idan babu wanda ya samu kashi 50% na ƙuri'u dole ne a sake zaɓe zagaye na biyu.

Duk da waɗannan matakan tsaro dai hare haren bam a Kandahar da safiyar yau sun halaka mutane biyu. Babban abokin hamaiyar Karzai, Abdullah Abdullah ya baiyana damuwarsa game da wannan hari.

"Ina mai matuƙar damuwa da tashe tashen hankulan na yau, game da batun tsaro, ko da yake a ga baki ɗaya ina da imani game da zaɓen, akwai rahotanni daga wasu sassa na ƙasar na hare hare amma duk da haka mutane sun nuna ƙarfin zuciya sun fito jefa ƙuri'arsu"

Sewar ɗan shekaru 34 yana daga cikin waɗanda suka fito jefa ƙuri'ar yana tsaye yana jiran a buɗe runfunan zaɓe, mintuna kusan 30 kafin a buɗe runfar a birnin Kabul, a cikin runfar kuma jami'an zaɓe na ci gaba da tsara takardun zaɓe, yayin da Sewar ke jiran zaɓen shugaban da yake ganin zai taimakawa jama'a.

Sewar yace koda yake yana daga cikin masu tashi da wuri. A 2004 yana daga cikin jama'a da suka yi jerin gwano a runfunan zaɓe don jefa ƙuri'unsu a zaɓen shugaban ƙasa na farko a ƙasar, inda a lokacin ma 'yan sanda suka yi ta sintiri don tsoron hari daga 'yan Taliban, koda yake duk da wannan Sewar yace ba ya tsoro.

"Su maƙiyan Afghanistan ne, suna son jawo hankalin al´umma ne akansu, amma na tabbata cewa 'yan sanda da sojoji zasu kare mu."

'Yan Taliban ɗin dai kwanaki kaɗan kafin zaɓen sun baiyana a fili cewa zasu tarwatsa wannan zaɓe da hare haren bam, suna masu neman cusa tsoro da fargaba a zukatan jama'a. Koda yake rundunar ƙasa da ƙasa a Afghanstan ta yi alkawarin ɗaukar dukkan matakai don ba da damar gudanar da wannan zaɓe cikin walwala, kamar yadda komandan rundunar Stanley McChrystal ya baiyana.

"Zamu yi iyakar ƙoƙarinmu, muna aiki tare da jami'an tsaro na Afghanistan, 'yan sanda da sojoji, zamu kuma yi anfani da jiragen sama don ƙara tabbatar da tsaro. Dakarunmu zasu kasance cikin shirin ko ta kwana idan sojin sa kai sun nemi dakatar da zaɓen, muna ɗaukar duk wasu matakai da suka dace don ganin cewa 'yan Afghanistan sun jefa kuri'unsu."

Sai dai kuma akwai wasu da suka ƙi fita jefa ƙuri'ar koda yake ba saboda tsoron harin bam ba, inji wannan mazaunin birnin Kabul.

"Sam bana tsoron harin bam, sai dai kawai saboda a zaɓen baya an yi maguɗi ne shi ya sa na zauna a gida."

A haƙiƙanin gaskiya akwai hujjoji dake nuna cewa an buga dubban katunan shaidar zama ɗan ƙasa na jabu, wanda ma ana iya sayensu a kasuwannin bayan fage. Dubban masu sa ido na gida da waje dai suna sa ido a wannan zaɓe, Ƙungiyar Tarayyar Turai ma ta tura tawagar, koda yake shugaban tawagar Gunter Mulack yace saboda dalilan tsaro ba dukkan gurare ba ne zasu iya zuwa.

"Muna a cikin ƙasa ne da yanzu haka take cikin yaƙi, inda kashi 75% na jama'arta basu iya karatu da rubutu ba, a irin hali da ake ciki muna fata cewa zaɓen zai gudana cikin 'yanci da walwala."

Mawallafa: Kai Küstner/Hauwa Abubakar Ajeje

Edita: Mohammad Nasiru Awal